Ghana ta bukaci ‘yan kasar da su guji tafiye-tafiye marasa mahimmanci zuwa Abuja

Gwamnatin Ghana ta gargadi ‘yan kasarta kan balaguro zuwa babban birnin tarayyar Najeriya Abuja saboda matsalar tsaro.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ranar Laraba ta ce gargadin ya biyo bayan mawuyacin hali da ake ciki a babban birnin kasar da kuma umarnin da hukumomi Najeriya suka bayar na a rufe otal-otal da ke gidajen kwana.
Sanarwar ta ta bukaci ‘yan kasar Ghana da dole sai sun shiga birnin Abuja da su tabbaatar sun dauki matakin kariya da taka tsan-tsan, inda ma’aikatar za ta ci gaba da sanya ido kan yadda al’umara ke ganuna tare da bayar da bayanai ga jama’a idan lamarin ya daidaita.”
Ana yawan tafiye-tafiye tsakanin Ghana da Najeriya, manyan kasashe biyu mafi karfin tattalin arziki a yammacin Afirka.
Gargadin kasashen yamma
Hakan na zuwa ne makonni bayan Amurka da wasu ofisoshin jakadancin kasashen waje sun yi gargadi game da tafiye-tafiye zuwa babban birnin Najeriya saboda barazanar ta’addanci.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta roki ‘yan kasar da su kwantar da hankulansu tana mai tabbatar musu da cewa jami’an tsaro na kokarin dakile duk wata barazanar ta’addanci.
©Rfi Hausa.