August 27, 2022

GDPn Nijeriya ya karu da kaso 3.54 cikin rubu’i na biyu a bana

GDPn Nijeriya ya karu da kaso 3.54 cikin rubu’i na biyu a bana
Hukumar kididdiga ta Nijeriya ta sanar da cewa, cikin rubu’i na biyu a bana, adadin karuwar ma’aunin tattalin arziki na GDP na kasar, ya kai kaso 3.54, wanda ya karu da kaso 0.43 idan aka kwatanta da na rubu’in farko na bana.
Hukumar wadda ta bayar da sanarwar a jiya ta ce, adadin ya riga ya karu ne cikin rubu’i 7 a jere, tun daga rubu’i na uku na shekarar 2020 har zuwa yanzu. ©(Maryam)

SHARE:
Noma da Kiwo 0 Replies to “GDPn Nijeriya ya karu da kaso 3.54 cikin rubu’i na biyu a bana”