June 3, 2024

Gawarwakin da aka gano a sansanin Jabalia sun kai 120 yayin da aka samu karin 50

Tawagar ceto Falasdinawa sun sake gano wasu gawarwaki 50 daga baraguzan sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza, lamarin da ya kawo adadin gawarwakin da aka kwato bayan janyewar sojojin Isra’ila daga yankin zuwa fiye da 120, kamar yadda tashar talabijin ta Press TV ta ruwaito.

Kamfanin dillancin labaran Wafa na kasar Falasdinu ya bayar da rahoton cewa, kungiyoyin agaji da na kare fararen hula sun kwato gawarwakin Falasdinawa 50 a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da ake ci gaba da neman mutane da dama da suka bace a cikin baraguzan gine-ginen da aka lalata a harin bama-bamai da Isra’ila ke yi.

Wannan na zuwa ne yayin da tuni kungiyoyin agaji suka kwato gawarwaki sama da 70 da suka hada da yara 20 a yankin.

Hakazalika majiyoyin lafiya a asibitin Kamal Adwan da ke garin Jablaia da ke arewacin Gaza sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, ma’aikatan agajin gaggawa da kungiyoyin kare hakkin farar hula sun kwato gawarwakin Falasdinawa sama da 120 daga baraguzan gine-gine da suka ruguje a Jabaliya. Har yanzu dai tarkace na ci gaba da gudana kwanaki biyu bayan da sojojin Isra’ila suka bar sansanin.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai gwamnatin kasar Isra’ila ta sanar da janyewa daga sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Gaza biyo bayan farmakin kwanaki 20 da ta kai a yankin wanda ya kai kusan 200 hare-hare ta sama.

A cewar hukumomin Falasdinu, farmakin ya lalata kashi 70 cikin 100 na Jabalia, wanda shi ne sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma a Gaza, kuma mazaunin Falasdinawa sama da 100,000.

Kafofin yada labarai daban-daban kuma, sun ambato Falasdinawa da suka koma sansanin bayan ficewar Isra’ila da bayyana yankin a matsayin “ba a iya gane shi ba” saboda irin barnar da ta’addancin Isra’ila ya yi.

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya, Philippe Lazzarini,  ya kuma saka hotunan “mafi firgita” na sansanin ‘yan gudun hijira na Jabalia, yana mai nuna alhinin irin barnar da harin da Isra’ila ta kai sansanin.

 

Mai Fassara:Hadiza Mohammed

®Press tv

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Gawarwakin da aka gano a sansanin Jabalia sun kai 120 yayin da aka samu karin 50”