September 2, 2021

Garkuwa da Mutane: ‘Yan sanda sun ceto malamin jami’a a Benuwai

Dagag Muhammad Bakir Muhammad
Hukumar yan sanda a jahar Benuwai sun tabbatar da kwato wani malamin jami’a a yau Alhamis. Malamin dai mai suna Dakta Godwin Kwanga ya kasance malami a jami’ar jaha ta Benuwai (BSU) da ke garin Makurdi haka kuma ya kasance tsohon ma’aikacin hukumar zabe ta INEC.
Jamiar hulda da jama’a na hukumar yan sandan jahar kuma mataimakiyar sufurtandan yan sanda katherine Anene tace malamin jamiar dai a ranar talata ya bar gurin sana’ar sa dake titin George Akume daga baya aka samu labarin sace shi ba tare da an san su waye ba haka kuma ba’a san inda aka kaishi ba.
Ta kuma kara da cewa tuni bayan aukuwar lamarin aka tura da jami’ai don bincike ta hakan ne ma aka samo motar malamin a ranar Talatar, baya da haka kuma jami’an suka cigaba da bincike.
Biyo bayan binciken na jami’an sun samu nasarar kai-ga-ci a yau Alhamis, inda suka gama tattara bayanan da suka nuna wanda aka sace din an aje shi ne a kauyen Tse-Anjov inda kuma suka shirya tsaf suka nufi kauyen, da farko yan bindigan sun yi musayar wuta da  jamian amma saidai jamian sun ci karfin su.
Bayan gumurzu na wasu lokuta yan sandan sun yi nasarar ceto wanda aka sace din kana sukuma yan bindigan sun tsere amma tare da raunukan harsasai
A bangaren ganima kuwa ‘yan sandan sun sami bindiga kirar Ak47 wacce ke dauke da harsasai haka kuma sun samu manyan harsasai wadanda basu gaza 43 ba tare da kuma motoci guda biyu kirar Kamri.
jamiar hulda jamar Katrine ta shawarci jama’a da su cigaba da bada hadin kai ga jami’an tsaro haka kuma su rika kai rahotanni da bayanai na motsin duk wasu bata gari.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Garkuwa da Mutane: ‘Yan sanda sun ceto malamin jami’a a Benuwai”