August 28, 2021

Garkuwa Da Mutane: An Damke Da Dama Yayin Kwato Dalibar KWASU

Daga Muhd Bakir Muhd

A satin da ya gabata masu garkuwa da muatene sukayi garkuwa da wata dalibar Jami’ar Jiha ta Kwara mai suna Khadijat Isiaq wacce ta kance dalibar aji uku a jami’ar, ita dai dalibar an yi garkuwa da ita ne aranar Lahadin da ta gabata.

Masu garkuwan dai sun nemi Naira miliyan 50 matsayin kudin fansa.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar bisa hadakar sauran hukumomin tsaro na musamman ta kaddamar da wani farmaki na musamman bisa aniyar kwato ta biyo bayan hakan kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu inda sukayi nasarar kwato ta da kuma kama a kallam mutum 6 daga cikin tawagar ta masu garkuwa da mutane.

Mai Magana da yawun hukumar ;yan sanda ta jihar Okasanmi Ajayi ya tabbatar da kwato dalibar inda kuma ya tabbatar da jinjina ga goyon baya da taimakon da suka samu daga Sufeto Janar na yan sanda, Mafarauta, ‘yan Baka da kuma hukumar makaranta,

Ya kuma kara da cewa sun damke mutum shida daga cikin masu garkuwa da mutanen inda suka same su da muggan makamai daban-daban ya kuma bayyana cewa zasu mika su kotu da zarar sun kamala binciken su.

Khadija da aka kwato an tabbatar da kasancewar ta cikin koshin lafiya, shugaban jami’ar ta KWASU Prof Muhammed Akanbi ya nuna farin cikin sa da godiya ga hukumar ta ‘yan sanda bisa jajircewa da kokarin su.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Garkuwa Da Mutane: An Damke Da Dama Yayin Kwato Dalibar KWASU”