January 25, 2023

GARAƁASA A WATAN RAJAB.

 

Annabi (S) yace: “Rajab watan gafartawa al’ummata ne, ku yawaita istigfari a cikin sa”.

Imam Musa Al-kazim (AS) yace: “Rajab wata ne mai girma, Allah maɗaukaki yana ninka kyawawan ayyuka a cikin sa, sannan yana goge munanan ayyuka”.

Imam Musa Al-kazim (AS) yace: “Rajab wani kogi ne a aljanna, da yafi nono fari, kuma yafi zuma zaƙi, wanda ya azumci rana ɗaya a wannan wata Allah zai shayar dashi daga wannan kogi”.
A wani hadisin kuma yace: “Wanda ya azumci rana ɗaya a watan Rajab za’a nisantar da wuta daga gare shi na tsawon tafiyan shekara guda, wanda kuma ya azumci kwanaki uku aljanna ta wajaba gare shi”.

Kwaɗaitarwa Akan Sadaka Da Taimakon Gajiyayyu.

Sahabbai sun tambayi Annabi (S) wanda bai samu ikon azumtar wannan ranaku ba me zai aikata domin samun wannan lada?
Sai Annabi (S) yace: “Yayi sadaka ga miskini, na rantse da wanda raina yake hannun sa zai samu ladan nan ko fiye”.

Ruwaya daga Ali ɗan Salim daga baban sa yace: “Na shiga wajen Sadiq (AS) a watan rajab, a yayin da ranakun suka kusa ƙarewa, sai yace: Ya salim shin kayi azumi a cikin wannan wata? Nace: A’a ya ɗan manzon Allah, sai yace min: Haƙiƙa lada da babu wanda yasan girman sa sai Allah ya wuce ka, domin wannan wata Allah ya girmama shi ya kuma ɗaukaka shi, sai nace ya ɗan manzon Allah shin idan na azumci abinda ya rage na daga ranakun watan zan samu dacewa? Sai yace: “Ya salim wanda ya azumci rana daya a ranakun ƙarshen wannan wata (azumin) zai amintar dashi daga tsananin magagin mutuwa da azaban ƙabari, wanda kuma ya azumci ranaku biyu na ƙarshen wannan wata zai samu dacewa akan siradi, wanda ya azumci ranaku uku na ranakun ƙarshen wannan wata Allah zai amintar dashi daga babban firgita, sannan za’a rubuta masa barranta daga wuta.

Falalan Umra A Watan Rajab.
Yazo cewa: Mustahabbi ne mai ƙarfi yin umra a wannan wata na rajab, cewa: yin umra a wannan wata yana biye da Hajji a falala.

Falalan Istigfari Da Hailala.
Ibnu Dawus ya ruwaito a Iqbal, daga Annabi (S) yace: “Wanda yace Astaghfirullah Allazi La’ilaha illahuwa, wahdahu la sharika lahu wa atubu ilaihi” Sau dari a rana, ya bishi da sadaka, Allah zai yi masa stanfi na rahama da gafara, wanda kuma ya karanta a rana sau dari hudu, Allah zai rubuta masa ladan shahidai 100, idan ya haɗu da Allah ranar kiyama, Ubangiji zaice masa ka roki dukkan abinda kake so, domin babu wani mai iko sai ni”.

Ruwaya daga Annabi (S) yace: “Wanda yace La’ilaha illallah sau 100, Allah zai rubuta masa kyawawan ayyuka 100, sannan za’a gina masa birane 100 a aljannah.

Falalan Karanta Suratu Tauhed (Qulhuwa)
Ibnu Dawus ya ruwaito a Iqbal mustahabbancin karanta Qulhuwa ƙafa 100, yana da falala mai yawa, wanda ya karanta a daren juma’an watan Rajab kafa 100, zai kasance yana haske a ranar Kiyãma zuwa Aljannah.

Kada ku manta dan uwan ku cikin addu’oin ku, Allah ya bamu dacewa.

@Emran Haruna Darussalam.

SHARE:
Makala 0 Replies to “GARAƁASA A WATAN RAJAB.”