June 30, 2022

Gani ga wane…

Daga: Baban Hadiza


Wata rana dila yanzaune a gefen tsauni, sai wani dutse ya gangaro daga sama ya fado masa a kan jela ta gutsire, yana haka sai ga wani dilan ya zo ya gan shi da gutsirarriyar jela, sai ya ce da shi: Me ya sa ka gutsire jelarka?
Sai ya ce: Na fi jin dadi a haka, ji nake yi kamar ina tashi sama domin dadi, wayyi dadi!

Nan ya rudi dilan nan har shi ma ya gutsire tasa jelarsa, sai bai ji dadin da aka fada masa ba ana ji ba, in ban da dan karen ciwo da yake shigarsa. Sai ya ce: Don me ya sa ka yi mini karya ka ce dadi ake ji?

Sai dilan nan ya ce: Idan ka fada wa sauran dilolin irin azabar da kake sha ba za su yanke jelolinsu ba, kuma za su rinka tsokanarmu.

Sai suka shiga ba wa sauran dolilin labarin irin irin dadin da suke ji da gutsirarriyar jela, da haka mafi yawan dilolin suka gutsittsire jalolinsu.
Daga baya kuma sai aka shiga yi wa duk wani dila da aka gani da doguwar jela izgili, ya zama abin zolaya.

To kwabo da kwabo, hala lamarin yake kasancewa a duk lokacin da fasadi ya game al’umma, sai a koma yi wa muminai izgili da imaninsu.

Ya zo a ruwaya cewa: Lokaci zai zo wa mutane da za a rinka aibata mumini da imaninsa, kamar yadda ake aibata fajiri da fajircinsa a yau, har a rinka cewa da mumini: Wai kai mutumin kirki!

Hakika batacciyar al’umma idan ta rasa abin da za ta aibata mumini da shi ko ta tuhume shi da shi, sai ta aibata shi da abin da yake shi ne mafi kyawu.

Irin yadda mutanen annabi Lud suka rinka yin izgili da cewa: Ku fitar da mutanen Lud daga garinku, wai su tsarkakkakkun mutane!

SHARE:
Tarbiyyan Yara, Tarbiyyar Ruhi A Musulunci 0 Replies to “Gani ga wane…”