December 5, 2023

Ganawa tsakanin kasashen Nijar da Rasha a birnin Yamai

Tawagar dake karkashin jagorancin mukadashin ministan tsaron Rasha janar kanal Lounous-Bek Evkourov na rangadin aiki tun ranar 3 zuwa 4 ga watan Disamban shekarar 2023 a Yamai, babban birnin kasar.

Inda a ranar ta jiya Litinin, wannan tawaga ta samu tattaunawa tare da takwarorinsu na kasar Nijar a karkashin jagorancin ministan tsaron kasar janar Salifou Modi. A tsakiyar wannan tattaunawa, karfafa dangantakar kasashen biyu a fannin tsaro da yaki da ta’addanci. Haka kuma, ganawar ta samu halartar manyan sojojin kasar Nijar da dama na matakai daban daban.

Jim kadan, bayan wannan zaman taro tsakanin manyan jami’an kasashen biyu, mista Evkourov da shi da jami’an dake rakiyarsa sun samu ganawa tare da shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, kuma shugaban kasa, janar Abdourahamane Tiani a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai.

A karshen wannan ganawa tare da shugaban kasar Nijar, mukadashin ministan tsaron kasar Rasha, ya jadadda goyon bayan kasarsa ga sabbin hukumomin Nijar a karkashin jagorancin CNSP bisa ga kokarin da suke na ganin kasar Nijar ta doshi hanyar ci gaba mai dorewa.

© CRI

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Ganawa tsakanin kasashen Nijar da Rasha a birnin Yamai”