May 18, 2024

G7 sun yi kira ga “Isra’ila” da ta mutunta dokokin kasa da kasa

Jaridar ahlulbaiti ta nakalto daga tashan Al-mayaden ta laranci cewar

A cikin wata wasika da dukkan kasashen G7 suka sanya wa hannu, ban da Amurka, tare da Australia, Koriya ta Kudu, New Zealand, Netherlands, Denmark, Sweden, da Finland, kasashen sun yi kira ga “Isra’ila” da ta mutunta dokokin kasa da kasa.

Kasashen yammacin duniya sun kuma bukaci “Isra’ila” da ta magance mummunan bala’in jin kai a Gaza. Har ila yau, sun bayyana rashin amincewarsu da “aikin soji na ci gaba da kai wa a Rafah” tare da yin kira ga “Isra’ila” da ta bar agajin jin kai ya isa ga jama’a “ta dukkan wuraren da suka dace, ciki har da na Rafah.”

Sun kuma bukaci gwamnatin Netanyahu da ta dauki karin matakai, kamar kokarin samar da “tsagaita wuta mai dorewa,” da samar da karin “fitarwa,” da kuma dawo da “lantarki, ruwa, da ayyukan sadarwa.”

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “G7 sun yi kira ga “Isra’ila” da ta mutunta dokokin kasa da kasa”