April 17, 2023

Fursinoni Falasdinwa Kimani 5,000 Ne Suke Tsare A Gidajen Yarin Yahudawan Sahyoniyya

Tashar talabijin ta Presstv a nan tehrana ta bayyana cewa rahoton wanda hukumar kula da al-amuran fursinonin Falasdinawa ta fitar a jiya Lahadi ya kara da cewa daga cikin fursinonin 4900 da suke tsare 31 daga cikinsu mata ne, sannan akwai yara yan kasashe da shekaru 18 ,160 suna tsare a gidajen yarin HKI.

Banda haka rahoton ya kara da cewa akwai fursinoni kimani dubu guda wadanda gwamnatin HKI tana tsare da su da sunan : Fursinonin harkokin gudanarwa’ , inda sukan tsare mutane na akalla wata 6 sannan su tsawaita shi bayan ko wata shida-shida har zuwa tsawon lokacinda suka ga dama.

Wannan fursinoni zasu ci gaba da kasancewa a tsare ba tare da an fada masu laifukan da suka aikata ba, ko kuma ba tare da an kaisu gaban kotu ba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Fursinoni Falasdinwa Kimani 5,000 Ne Suke Tsare A Gidajen Yarin Yahudawan Sahyoniyya”