November 23, 2023

Fiye Da Makamai Masu Linzami 50 Hizbullah Ta Harba Akan Sansanonin Israila

 

Kafafen watsa labarun israila sun ce da’irar da Hizbullah take kai wa hari da makamai masu linzami ta kara fadada a wannan Alhamis.

Mai Magana da yawun sojojin mamaya na israila ya ce; Abinda yake faruwa akan iyakar Arewa yana nuni da kara tabarbarewar al’amurra, sannan kuma zai iya karuwa.”

Kafafen watsa labarun Israila sun ce; Tun da safiyar Alhamsi ake ta jin karar jiniyar gargadi a kan iyaka da Lebanon.

Ita kuwa tashar talabijin din “Channel 13” ta israila ta ce; Babu wani yanki da makamai masu linzami na Hizbullah ba sauka ba a Arewa, kuma babu kakkautawa.”

Tashar talabijin din ta cigaba da cewa; Nisan yankin da makamai masu linzamin su ka isa sun kai kusa da garin Safad.

Kungiyar Hizbullah ta fitar da jerin bayanai akan hare-haren da ta kai wa sansanonin sojan mamayar israla dake kan iyaka. Daga ciki da akwai kai hari da makami na musamman akan wani gida da sojojin mamaya 4 su ka shiga a sansanin ‘yan share wuri zauna na ‘almanarah” tare da kashe su baki daya, da kuma rusa gidan da su ka shiga.

Bugu da kari gwagwarmayar musulunci ta Hizbullah ta sanar da harba makamai masu linzami samfurin katiusha 48 akan sansanonin soja dake yankuna Jalilul-A’ala, da wasu cibiyoyin leken asiri na ‘yan mamaya.

 

©V.O.H

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Fiye Da Makamai Masu Linzami 50 Hizbullah Ta Harba Akan Sansanonin Israila”