August 10, 2021

FASSARAR HADISIN KISA’I

Fassarar Yakub Salisu Dady
Daga Jabir ɗan Abdullahi Al’ansari yace: Naji Fatimatuz zahra (a.s) ƴar Manzon Allah (s.a.w.w) tana cewa:
    Babana manzon Allah (s) ya shigo wajena wata rana, sai yace: Assalamu alaiki ya fatima, sai nace: wa’alaikas salamu ya babana, yace ina jin gajiya a jikina, sai nace masa: ina nema maka tsarin Allah da gajiya, sai yace: ya Fatima kawo min bargo (saƙar yamen) ki rifeni dashi. Sai nazo da bargon na lulluɓeshi dashi na zauna ina kallonsa, saiga fuskarsa (s.a.w.w) tana haske da walwali kamar wata a cikarsa.
    Bayan ɗan lokaci saiga ɗana (Imam)
Hasan (a.s) ya shigo, sai yace” Amincin Allah ya tabbata a gareki ba ummata, sai nace masa Anincin Allah ya tabbata gareka ya hasken idanuna… Sai yace ya ummata ni ina jin kamshi mai daɗi a wurinki, kamar kamshin kakana Manzon Allah (s). Sai nace masa Eh kakanka yana ƙasan bargo, sai Hassan yazo wajan bargon yace: Amincin Allah ya tabbata gareka ya kakana ya Rasulallah, shin kayi min izini na shigo cikin bargon ?, sai (Annabi) yace: Amincin Allah ya tabbata gareka ya ɗana ya ma’abocin ƙoramata  nayi maka izini ka shigo, sai ya shiga ciki tare dashi.
Bayan ɗan lokaci saiga ɗana (Imam) Hussain  (a.s), sai yace” Amincin Allah ya tabbata a gareki ba ummata, sai nace masa Anincin Allah ya tabbata gareka ya hasken idanuna… Sai yace ya ummata ni ina jin kamshi mai daɗi a wurinki, kamar kamshin kakana Manzon Allah (s). Sai nace masa Eh kakanka yana ƙasan bargo tare da ɗan uwanka, sai Hussain ya matsa wajan bargon yace: Amincin Allah ya tabbata gareka ya kakana ya zaɓaɓɓan Allah, shin kayi min izini na kasance tare daku cikin bargon ?, sai (Annabi) yace: Amincin Allah ya tabbata gareka ya ɗana ya macecin Al’ummata nayi maka izini ka shigo, sai ya shiga ciki tare dasu.
A daidai lokacin saiga Baban Hasan (Imamu Ali (a.s) ɗan Abi ɗalib ya shigo, sai yace: Amincin Allah ya tabbata gareki ya ɗiyar Manzon Allah, sai nace masa, Amincin Allah ya tabbata gareka ya baban hasan ya Amiral Muminin, sai yace: ya fatima ina jin ƙamshi mai daɗi kamar ƙamshin ɗan uwana ɗan baffana Manzon Allah (s.a.w.w). Sai nace masa: Eh shine tareda ƴaƴanka a kasan bargo, sai (Imam) Ali ya kusanci bargon yace: Amincin Allah ya tabbata gareka ya Manzon Allah, shin kayi min izini na kasance tare daku cikin bargon ?, sai (Annabi) yace: Amincin Allah ya tabbata gareka ya ɗan uwana ya magajina kuma khalifana maɗaukin tutana, nayi maka izini ka shigo, sai Ali ya shiga tare dasu.
  Sai nima (fatima) na ƙaraso nace: Amincin Allah ya tabbata gareka ya babana shin kayi min izini na kasance tare daku a cikin bargon ?, sai yace: Amincin Allah ya tabbata gareki ya ƴata ya tsokar jikina nayi miki izinin shigowa, saina shiga cikinsu.
  A lokacin da muka gama shiga, sai Babana manzon Allah ya kama gefen bargon, sai ya ɗaga hannunsa na dama zuwa sama… Sannan yace: Ya Allah wadan nan sune Iyalan gidana kuma keɓantattuna … Namansu namanane, jininsu jininane, duk abinda ya cutar dasu ya cutar dani, duk abinda ya baƙanta musu ya baƙanta min, ina faɗa da wanda yake fada dasu, ina zaman lafiya da wanda yake zaman lafiya dasu, ina adawa da masu adawa dasu, ina son mai sonsu, su dagani suke nima dagasu nake… Ka sanya salatinka da albarkarka da rahmarka da gafararka da yardarka akaina da kansu kuma ka tafiyar da ƙazanta daga garesu ka tsarkakesu tsarkakewa.
  Sai Allah (s.w.t) mai girma da daukaka yace: ya mala’ikuna da mazauna sammaina, Lallai ban halicci sama tsayayya ba ko kasa ba ko wata mai haske ba ko rana mai haskakawa ba kwale-kwale mai yawo ba ko kogi mai gudu ba ko … Sai dan soyayya ga waɗannan mutum biyar ɗin da suke ƙasan bargo. Sai Amintacce (mala’ika) jabrilu yace: ya ubangiji to suwaye a kasan bargon ? Sai Allah yace: sune iyalan gidan annabta kuma maɓuɓɓugar sakona, sune fatima da mahaifinta da mijinta da ƴaƴanta. Sai mala’ika jibrilu yace: ya ubangiji shin kayi min izini na suka kasa na zama na shidansu ?, sai Allah yace: nayima.
  Sai Mala’ika jabrilu ya sauko kasa yace: Amincin Allah ya tabbata gareka ya manzon Allah, Allah yana gaisheka kuma ya keɓance ka da gaisuwa,  kuma yanace maka: ina rantsuwa da daukakata da girmana lallai ban halicci sama tsayayya ba ko kasa ba ko wata mai haske ba ko rana mai haskakawa ba kwale-kwale mai yawo ba ko kogi mai gudu ba ko … Sai dan soyayyarsa gareku, kuma yayi min izini na shiga (bargo) tare daku, shin kayi min izinin shiga ya manzon Allah ?, sai manzon Allah yace: Amincin Allah ya tabbata gareka ya ma’abocin wahayin Allah, Eh nayi maka izinin shiga, sai jibrilu ya shiga cikinsu ƙasan bargo, sai yacema babana: lallai Allah yayi muku wahayi yana cewa:   ”’LALLAI ALLAH YAYI NUFIN TAFIYAR DA ƘAZANTA DAGA GAREKU YAKU MA’ABOTA BABBAN GIDA, KUMA YA TSARKAKEKU TSARKAKEWA”’. Sai (Imam) Ali yacema babana (s.a w.w) ya manzon Allah ka faɗa mana dangane da zamanmu anan ƙasan bargo na daga falala a wajan Allah ?, sai Annabi yace: Ina rantsuwa da wanda ya aikoni da gaskiya a matsayin Annabi, kuma ya zaɓeni da babban saƙo, ba’a ambaci wannan labarin namu ba a taro cikin taruka na mazauna doron ƙasan kuma cikinsa akwai gungu na ƴan shi’armu da masoyanmu face an saukar musu da rahma kuma mala’iku su kewaye su suna nema musu gafara harsu watse.
  Sai Ali (a.s) yace: Na rantse da ubangijin ka’aba mun rabauta muda ƴan shi’armu
   Sai babana manzon Allah (s) yace: Ina rantsuwa da wanda ya aikoni da gaskiya a matsayin Annabi, kuma ya zaɓeni da babban saƙo, ba’a ambaci wannan labarin namu ba a taro cikin taruka na mazauna doron ƙasan kuma cikinsa akwai gungu na ƴan shi’armu da masoyanmu kuma cikinsu akwai mai bakin ciki da damuwa face Allah ya yaye masa bakin cikinsa da damuwarsa, ko kuma mai neman biyan wata buƙata face Allah ya biya masa buƙatarsa.
   Sai (Imam) Ali (a.s) yace: to lallai mun rabauta kuma munyi farin ciki hakama ƴan shi’armu sun rabauta kuma sunyi farin ciki a duniya da lahira na rantse da Ubangijin ka’aba.
       Ruwayar tazo a littafin Awalimul ulum na sheikh Abdullah ɗan nurullah Albahrani da isnadi ingatacce daga (sahabi) Jabir ɗan Abdullah Ansari.
SHARE:
Makala 0 Replies to “FASSARAR HADISIN KISA’I”