October 13, 2021

Fashewar tankar Mai ya haifar da rasa rayuka a Adamawa

Daga Shayibu Billiri


Rahoton dai ya nuna cewa a kalla mutane 5 ne suka rasa rayukan su bayan fashewar tankar, lamarin wanda ya faru a garin Mubi da ke jahar Adamawa ya faru ne da safiyar yau Laraba.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa lamarin ya fara ne tun safiyar yau a gidan mai sakamakon juyen Man fetur kai tsaye daga tankar zuwa kanana da manyan jarakuna a kasuwar Gyela.

Mazauna yankin sun shaida cewa a kalla mutane 5 ne suka rasa rayukan su a sanadin faruwar al’amarin. Wani mutum ya shaida cewa mutum 3 daga cikin mutane 5 din yan uwan juna ne daga dangi daya.

Bawan Allahn ya kuma kara da cewa baburan adaidaita sahu da suke ajiye kusa da tankar duk sun kone.

Shugaban bangaren ujila a jahar, Dr. Muhammad Suleiman ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace mutane 3 sun rasa rayukan su inda wasu 2 kuma ke gadajen asibiti domin magani duk A sanadin faruwar lamarin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Fashewar tankar Mai ya haifar da rasa rayuka a Adamawa”