November 30, 2022

Fashewa A Wata Makarantar Addini Ta Yi Ajalin Dalibai 16 A Afghanistan

Rahotanni daga Afghanistan na cewa daliban makarantar addini 16 ne suka rasa rayukansu biyo bayan wata fashewa da ta afku yau Laraba.
Harin ya faru ne a Lardin Samangan inda dalibai da dama suka hallara domin yin sallar Azahar.

Ko baya ga wadanda suka rasun da akwai wasu sama da mutum 25 akasarinsu yara da suka ji rauni.

Har zuwa lokacin fasara wadanan labaren babu wata kungiya da ta dauki lhakin kai harin.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ire iren wadanan hare haren ke rutsawa da fararen hula tun bayan da kungiyar Taliban ta karbe mulki a wannan kasa ta Afganistan a watan Agustan bara

 

©Hausa TV.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Fashewa A Wata Makarantar Addini Ta Yi Ajalin Dalibai 16 A Afghanistan”