May 6, 2023
Farashin Danyen Mai Ya Tashi Bayan Asarar Da Aka Tafka A Wannan Mako

Farashin man fetur ya tashi a jiya Juma’a, bayan da aka samu hasarar da aka samu a wannan makon, sakamakon fargabar koma bayan tattalin arziki, wanda zai shafi bukatar danyen mai.
Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a jiya farashin danyen mai na US West Texas Intermediate ya tashi da kashi 1.27% zuwa dala 69.43 a kan kowace ganga kan ganga daya.
Yayin da farshin danyen mai na Brent ya tashi da kashi 1.32% zuwa dala 73.46, a cewar bayanan hukumar Bloomberg.
Duk da tashin da farashin na danyen mai ya yi a jiya, amma har yanzu kamfanoni na ci gaba da tafka asara, tun bayan rikitowar farashin a kasuwannin duniya a cikin ‘yan kwanakin nan