Faransa zata hana yan makaranta sanya abaya wanda wasu musulmi suke sawa a makarantun gwamnati a kasar.

Gwamnatin kasar faransa ta bada sanarwan cewa zata samar da doka wacce zata hana yan makaranta sanya abaya wanda wasu musulmi suke sawa a makarantun gwamnati a kasar.
Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa kafin haka gwamnatin kasar tana hana yan makaranta sanay hajabi mai rufe kai a makarantun kasar sannan ta hana sanay duk wata alamu ta addini a makarantun kasar.
Labarin ya kara da cewa ministan ilmi na kasar Gabriel Attal ya bayyana cewa a shekarar karatu mai zuwa gwamnatin kasar zata hannu yan makaranta sanya duk wani abu wanda zai sa a gane addinin dan makaranta a aji daga ciki har da abaya wanda wasu mata musulmi suke sawa a kasar.
Kasar faransa dai tana da musulmi kimani miliyon 5 kuma babban kungiyar musulmi ta kasar The French Council of Muslim Faith (CFCM), kaya saw aba alama ce ga wani addini ba don haka bata ga dalilin da gwamnatin kasar faransa zata dauki wannan matakin ba.
A shekara ta 2004 ta haramta sanya hijabi mai rufe kai sannan a shekara ta 2010 ta hana sanya kellen rufe fuskan da mata musulmi suke sawa