November 25, 2023

Falasdinawa Suna Murnar Sako Mata 39 Ta Hanyar Musayar Fursunoni ,

 

Musayar fursunonin da aka yi a jiya Juma’a a tsakanin HKI da kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hmas, an sako matan Falasdinawa 39 daga kurkuku.

Sakin fursunonin na jiya shi ne zango na farko a tsarin da aka yi a karkashin tsagaita wuta da zai dauki kwanaki 4. Daga cikin wadanda aka saki din a jiya da akwai karamin yaro namiji guda daya da suke a kurkukun Aufar.

An rika yin kabbarori a masallatan yankin Jenin da sansanoninta na Falasdinawa a matsayin nuna murna da sakin fursunonin.

Daga cikin matan da aka saki da akwai Malak da aka kama tana da shekaru 16 a lokacin tana kan hanyar zuwa makaranta a 2016, a yankin Babul-Amud dake tsohon birnin Kudus.

 

©V.O.H

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Falasdinawa Suna Murnar Sako Mata 39 Ta Hanyar Musayar Fursunoni ,”