October 20, 2021

END SARS: ‘Yan sanda sun cafke wasu matasa da suka fito zagayen tunawa da waki’ar Lekki

Daga Muhammad Bakir Muhammad


Rahotanni dake zuwa mana yanzu haka daga yankin Lekki dake jihar Legas na nuna cewa sama motocin ‘yan sanda 30 ne jibge a yankin na Lekki don tabbatar da tsaro da kuma kwantar da tarzoma a yankin.

Rahoton ya nuna cewa ‘yan sandan sun cafke wasu mutane da suka fito zagayen nuna rashin amincewa da abinda ya faru a rana mai kamar ta yau na shekarar da ta gabata.

A shekarar da ta gabata din dai an samu sabanin juna tsakanin jami’an tsaro da matasan da suka fito zanga-zangar neman dakatar da rundunar ‘yan sanda ta musamman wacce aka fi sani da SARS, inda jami’an tsaron suka farmaki wasu daga matasan wanda hakan yayi sanadiyyar rasa rayukan wasu daga cikin su.

A rahoton da ya zo mana a yau ya nuna cewa ‘yan sandan sun cafke wasu matasan da suka fito zanga-zanga na tunawa da abin da ya faru inda kuma suke rike da fastoci, ‘yan sandan sun cafke matasan inda kuma suka yi awun gaba da su.

Kafin faruwar lamarin, rahoto ya nuna cewa hukumar ‘yan sanda ta fitar da sanarwar jan kunne da gargadi kan kada wanda ya bayyana a titi da nufin zanga-zanga ko ta da tarzoma.

 

Ga kadan daga yadda lamarin ya kasance….

 

 

 

SHARE:
Labarin CIkin Hotuna, Rahotanni 0 Replies to “END SARS: ‘Yan sanda sun cafke wasu matasa da suka fito zagayen tunawa da waki’ar Lekki”