February 17, 2023

El-Rufai ya umarci al’ummar jihar Kaduna su ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗi

Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya umarci al’ummar jihar da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na naira 500 da 1000 bayan da shugaba Buhari ya jaddada matsayin Babban Bankin ƙasar na soke amfani da kuɗin.

A wani jawabi da gwamnan ya yi ga al’ummar jihar a jiya Alhamis, jawabin da ke zama kamar na ƙalubalantar shugaban ƙasar, ya bayyana shirin canja kuɗin a matsayin wani makami da jiga-jigan jam’iyya mai mulki da mkusantan Shugaba Buhari suka ɓullo da shi domin dakatar da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu nasara a zaben 25 ga watan nan na Fabrairu.

Gwamnan ya bayyana shirin a matsayin na rashin imani, wanda ya haddasa talakawan ƙasar tsananin wahala, waɗanda ya ce su ne shirin ya tagayyara.

Ya ce shugabancin Babban bankin ƙasar, CBN, ya yaudari Shugaba Buhari da cewa an ɓullo da shirin ne da nufin daƙile ‘yan siyasa da suka tara maƙudan kuɗade domin sayen ƙuri’a lokacin zaɓe.

Gwamnan y bai wa al’ummar jihar tabbacin su ci gaba da amfani da takardun kuɗin kamar yadda ya ce Kotun Kolin kasar ta bayar da umarni.

Ya ce babu wani wa’adi da zai sa kuɗin su daina aiki, yana mai umartar jama’a su ci gaba da amfani da kuɗin, inda ya ce bayan zaɓe shi da sauran ‘yan majalisa zaɓaɓɓu da hukumomin gargajiya za su tattara kuɗin daga hannun jama’a su mika su ga Babban Bankin domin a sauya su.

Ya ce doka ta tabbatar da cewa ko da nan da shekara 100 ne, duk lokacin da aka kai tohon kuɗi ɓ dole ya sauya ya bayar da sabo.

©Bbc

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “El-Rufai ya umarci al’ummar jihar Kaduna su ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗi”