October 5, 2021

EFCC TA SAKI MAI ‘DAKIN GWAMNAN JAHAR KANO

Isah Musa Muhammad


Mai dakin gwamnan jahar Kano, Dr. Hafsar Umar Ganduje ta samu kubuta daga hannun hukumar yaki da cin hanci da kuma yin zagon kasa ga tattalin arziki ta kasa wato EFCC bayan share tsahon awanni da dama a hannun su.

Kama mai dakin gwamnan Kano din ya biyo bayan kin amsa gayyatar girmamawa da hukumar ta EFCC ta yi mata, wanda ake zarginta da wani laifi da ya shafi filaye.

Dr. Hafsat ta ki amsa gayyatar hukumar ne kan zargin da suke yi mata na karar da dan ta ya shigar a kanta.

Dr. Hafsat din dai an sake ta ne bisa bukatar hakan da mijin ta Gwamnan jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi.

Tun a karon farko dai rahotanni sun nuna cewa gwamnan ne yayi rakiya ga mai dakin nasa zuwa helkwatan na EFCC, kana kuma yayi ruwa da tsaki wurin sakin ta.

Sun dawo garin Kano ne daga birnin Abuja, a yayin da suka sauka a filin jirgi na Malam Aminu Kano a yau Talata.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “EFCC TA SAKI MAI ‘DAKIN GWAMNAN JAHAR KANO”