September 14, 2021

EFCC na shirye-shiryen kama mai ɗakin gwamnan Kano

Daga Baba Abdulƙadir
Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon ƙasa ta EFCC akan zargin da yake yi mata da almundahana da kuma azurta kanta ta hanyoyin da basu dace ba.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewar Tuni hukumar EFCC ta aikewa da Hafsat Ganduje mai dakin Gwamnan Kano da goron gayyata domin amsa tambayoyi kan zargin amma taki amsa gayyata, ba kuma tare da ta bayar da wani uzuri a rubuce ba.
A cikin wasikar da Abdulaziz Ganduje ya aikewa da EFCC ta shafi badakalar filaye da kuma kudade. Sai dai kakakin hukumar EFCC Wilson Uwujaren yaki cewa komai game da batun da aka yi masa tambaya akai.
Sai dai wata majiya daga hukumar ta EFCC ta bayyana cewa tuni jami’an hukumar su ka fara shirye-shiryen kama Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ɗin muddin ta ƙi mutunta gayyatar.
Idan ba a manta ba, a baya ma an zargi Gwamnan Kano Alhaji Abdullahi Umar Ganduje da yin badakala ta sama da dalar Amurka miliyan biyar, inda aka nuno shi a wani faifan bidiyo yana karbar dalar Amurka daga cikin kudaden ‘yan kwangila, Gwamnan dai ya karyata bidiyon tare da kai karar jaridar Daily Nigerian da mawallafinta Jaafar Jaafar gaban kotu game da batun bidiyon Dala.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “EFCC na shirye-shiryen kama mai ɗakin gwamnan Kano”