September 25, 2021

Duniyar Musulunci Ta Yi Babban Rashi…

INNALILLAH WA INNA ILAIHI RAJI’UN

Allah ya yiwa babban Malami masanin irfani da falsafa rasuwa Ayatullah Sheikh Hassan Zada Amuli yana da shekaru 94, shekarun da yayi su wajen hidimtawa mazhabin nan na Imaman shiriya.

TAKAITACCEN RAYUWAR SHI
Sheikh Hassan zada Amuli ya kasance malami ne na falsafa kuma masani a fannonin ilimi da dama, ya wallafa litattafai masu tarin yawa, anayi masa lakabi da arifi ma’abocin fannoni masu yawa, kamar yadda yayi fice wajen adabi kuma babban malami ne a hauzar ilimi.

An haifi shehin Malamin ne a shekarata 1306 bayan hijira a Iran, wanda ya fara neman ilimi a shekarar 1328 har zuwa lokacin daya koma Tehran domin ci gaba da karatun shi na hauza a makarantar Hajj Abul-fathi, Daga cikin Malaman da yayi karatu a wajen su akwai Muhammad Taqiyyul Amuli, Almirza mahdi Al-kamsha’iy, Almirza Abul-Hasan Ash-sha’arani da Abul Hasan Rafi’il Kazwini.

A shekarar 1340 ne yayi hijira zuwa birnin Qom, inda ya karanci ilimin Hikima da tafsiri da sauran ilimummuka a wajen Sayyid Muhammad Hussein Tabattaba’i da Uztaz Muhammad Hassan Al-ilahi da Sayyid Al-Kadi da kuma sayyid Hadiyyul Kadi.

Bayan wannan ne ya fara bada ilimummukan Hikima,irfani da tafsiri, haka kuma ya bada muhimmanci a yabo da yaren farisi da kuma larabci.

KADAN DAGA ABINDA AKACE GAME DASHI
Sheikh Abul Hasan Ash-sha’arani yace: Sheikh Hassan zada shugaban mune, kuma tauraron addini.
Sayyid Muhammad Hussein Tabataba’i yace: Babu wanda yasan Allama Hassan zada hakikanin sani sai Sahibul Asr wazzaman “Imam Mahdi ” (Atfs).

Yana da litattafan daya wallafa dayawa a bangaren ilimin irfani da falsafa da fikihu da ilimin taurari da sauran su.

Allah ya lullube shi da rahamar sa.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Duniyar Musulunci Ta Yi Babban Rashi…”