August 29, 2023

Duk Wani Kisa Da Isra’ila Za Ta Aikata A Labanon, Zai Fuskanci Kakkausan Martani

 

Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon ya yi gargadin cewa duk wani yunkuri na kisan gilla da Isra’ila za ta yi a doron kasar Labanon, za ta fuskanci martani “mai karfi”.

Sayyid Hassan Nasrallah ya bayyana hakan ne a yayin wani jawabi kai tsaye da aka watsa ta gidan talabijin daga birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon a yammacin jiya Litinin, yayin da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru shida da nasarar ‘yantar da kasar Lebanon a karo na biyu.

A ranar 28 ga watan Agustan shekarar 2017 ne sojojin kasar Labanon da mayakan Hizbullah suka ‘yantar da iyakokin kasar daga hannun ‘yan ta’addar Daesh da makamantansu a ranar 28 ga watan Agustan shekarar 2017.

A baya bayan nan, Sayyid Nasrallah ya kira taron ‘yantar da kasa na biyu bayan samun ‘yanci na farko a shekara ta 2000, lokacin da kungiyar Hizbullah tare da sauran kungiyoyin gwagwarmaya na kasar Lebanon suka tilastawa sojojin mamaya na Isra’ila janyewa daga kudancin Lebanon da yankin Beka ta Yamma.

A yayin jawabin nasa na ranar litinin, Nasrallah ya ce Isra’ila ta yi ta kashe-kashe da dama a tsawon shekaru, amma ba ta iya raunana tsayin daka na ‘yan gwagwarmaya ba.

 

©voh

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Duk Wani Kisa Da Isra’ila Za Ta Aikata A Labanon, Zai Fuskanci Kakkausan Martani”