January 28, 2024

Dubun dubatar masu zanga-zanga a Isra’ila na neman Netanyahu ya sauka daga mulki

dubban mutane sun yi zanga-zanga a Isra’ila don neman Netanyahu ya sauka daga mulki, a gudanar da zabe.

Netanyahu yana shan matsin lamba sosai daga Isra’ilawa saboda gazawarsa wajen ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

Dubban Isra’ilawa sun gudanar da zanga-zanga a birane daban-daban, inda suke kira a rusa gwamnati a daidai lokacin da iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza suke nasu gangamin a kofar gidan Firaiminista Benjamin Netanyahu don neman ya sauka daga mulki.

“Dubban Isra’ilawa sun yi zanga-zanga a birnin Haifa, a mahadar Horev, domin kyamar gwamnati, inda suka bukaci a gudanar da zabe cikin gaggawa,” a cewar jaridar Yedioth Ahronoth. “An soma gangamiin ne daga yankin Carmel na birnin Haifa zuwa mahadar Horev da ke tsakiyar birnin

A birnin Kfar Saba, kusa da Tel Aviv, daruruwan mutane sun yi zanga-zanga dauke da kwalaye da aka rubuta “A Gudanar Da Zabe Yanzu,” in ji jaridar.

Masu zanga-zangar sun nemi a kori gwamnatin Netanyahu sannan a gudanar da zabe ba tare da bata lokaci ba.

Matsin lamba

Netanyahu yana cigaba da shan matsin lamba sosai daga Isra’ilawa saboda gazawarsa wajen ganin an sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza ba tare da ko kwarzane ba.

Gomman iyalan mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza sun gudanar da zanga-zanga a gaban gidan Netanyahu a birnin Caesarea (arewa) inda suka nemi ya sa a sako su.

©Jaridar Yedioth Ahronoth

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Dubun dubatar masu zanga-zanga a Isra’ila na neman Netanyahu ya sauka daga mulki”