January 8, 2023

​Dubban Yahudawan Sahyoniyya Sun Fito Zanga-Zangar Yin Allawadai Da Gwamnatin Natanyaho

 

Dubban yahudawan sahyoniyya sun fito zanga-zangar yin allawadai da gwamnatin Natanyahu mai wuce gona da iri a birnin Tel-avib babban birnin haramtacciyar kasar.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kakafayen yada labarai na yahudawan na cewa yahudawan wadanda suke ganin gwamnatin Natanyahu ce gwamnati mafi muni da kuma wuce gona da iri a tarihin hki.

A cikin watan Dicemban na shekarar data gabata ne Natanyahu yay i rantsuwar kama aiki a matsayin firari ministan HKI amma tare da hadin da yahudawa masu tsatsauran ra’ayi wadanda masana da dama suna ganin zasu kai yahudawan su baro a inda ba zasu iya fiddasu ba.

Da zaran gwamnatin ta fara aiki ne ministan tsaron cikin na gwamnatin HKI ya keta hurumin masallacin al-aksa tare da wasu mago bayansa, inda suka shiga masallacin da takalmansu suka kuma tsaye a ciki na kimani rubi’in sa’a.

Kasashen larabawa da musulmi da dama sun yi allawadai da keta hurumin masallacin wanda ministan yayi, sun kuma bayyana gwamnatin Natanyahu a wannan karon a matsayin wacce zata iya tada fitinan da ya hudawan basu taba ganin irin ta ba.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Dubban Yahudawan Sahyoniyya Sun Fito Zanga-Zangar Yin Allawadai Da Gwamnatin Natanyaho”