September 28, 2023

DSS Sun kama Dan Jarida A Filin Jirgin Sama Akan Hanyarsa Ta Zuwa Umrah

Wasu jami’an hukumar tsaron farin kaya (DSS) sun cafke babban editan fitacciyar jaridar Hausa ta Almizan, Malam Ibrahim Musa a Kano.

Ibrahim  Musa wanda ke kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya don gudanar da ibadar Umrah, lokacin da aka kama shi yana tare da rakiyar wata ‘yar uwarsa, Binta Sulaiman.

Jami’an tsaron sirrin na DSS sun dauke shi a filin jirgin saman Aminu Kano da safiyar Laraba.

Da yake magana a madadin ‘yan uwan editan na Almizan da ya shiga hannun, Abdullahi Usman, babu wani dalili da jami’an tsaron da suka ba iyalansa dangane da kamen.

A halin da ake ciki zuwa yanzu babu wani sanarwa daga hukumar DSS ta fitar dangane da kamun Babban Editan jaridar Al-mizan.

 

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “DSS Sun kama Dan Jarida A Filin Jirgin Sama Akan Hanyarsa Ta Zuwa Umrah”