September 5, 2021

Dokar Dakile Matsalar Tsaro: Al’ummar Jihohin Zamfara, Kaduna, Niger da Katsina sun Koka

Daga Abbass Manga 

A yan kwanakin da suka gabata gwamnonin jahohin Arewa ta yamma sun dau tsauraran matakai don dakile matsalar tsaro da ya dade yana addabar yankin.
Matakan dai sun hada da hana cin kasuwannin mako, safarar dabbobi, harkokin yan bumburutu, zirga-zirgan babura dasauran su.
Koda dai matakan nasu kwalliya ce ta biya kudin sabulu, amma a gefe gudan sai kuma wata sabuwar matsalar taltalin arziki ta kunno kai wanda ta jefa dayawa daga mutanen yankunan cikin halin kakani-kayi.
Tun bayan sanar da matakin da gwamnonin suka dauka, rayuwar mutanen da ke rayuwa a yankunan ya canza musamman ta fuskar taltalin arziki inda wakilan mu suka tattara bayanai daga yankunan kuma al’ummar da ke rayuwa a yankuna sun nuna matakan a matsayin tsauraran matakai.
Kana kuma sun nuna cewa illar matakan ba a iya kawunan su ya tsaya ba, ta shafi garuruwa da kananan kauyuka dake makobtaka dasu.
Rahotannin sun nuna cewa a yayin da farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi yayi tashin doran zabi ya haifar da nakasu a mutane da dama musamman masu kananan sana’o’i haka zalika manoma suna wahala wurin samun daman kai kayayyakin su zuwa kasuwanni domin sayarwa sanadin babu babura da sauran ababen hawa da zasuyi amfani dasu.
Sun bayyana cewa ko da wadannan matakai sun taka rawar gani wurin dakile matsalolin na tsaro to a bangare guda kuma tana da illoli da barazana ga rayukan al’umma ganin yadda gwamnati bata samar da wani yanayi da zai tallafe su ko ya rage masu radaddin halin da suka tsinci kansu ba.

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Dokar Dakile Matsalar Tsaro: Al’ummar Jihohin Zamfara, Kaduna, Niger da Katsina sun Koka”