November 30, 2021

Davido ya yi karin kan haske yadda gidajen marayu zasu cike tallafin sa na Miliyan 250

Aliyu Abdullahi


Shahararren mawakin Nijeriya, David Adedeji Adeleke wadda aka fi sani da “Davido” ya yi karin haske da cikakken bayani kan yadda gidajen marayu zasu iya samun tallafin sa na Naira miliyan 250.

A wani bayani da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta, mawakin ya bayyana cewa gidajen marayu wadanda gwamnatin kasa ta san da zaman su ne kadai zasu amfana da tallafin.

A yan kwanakin da suka gabata, mawakin ya tara kudade da adadin su ya kai kimanin miliyan 200 a cikin kwanaki biyu kacal, hakan kuwa ya biyo bayan wani rubutu da ya wallafa a shafinsa cewa abokansa su tura masa kudi don taya shi murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Bayan samun wadannan kudi da adadin su ya kai naira miliyan 200, mawakin ya kara naira miliyan 50 kan naira miliyan 200 din, sannan kuma ya sanar cewa zai bada tallafin kudin ga gidajen marayu a fadin kasar.

Daga karshe ya Samar da kwamitin mutane 5, wanda suka hada da farfesoshi 3 wadanda zasu gudanar da aiyuka na raba kudin.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Davido ya yi karin kan haske yadda gidajen marayu zasu cike tallafin sa na Miliyan 250”