November 19, 2022

DAURA GA WAKILAN RASSA NA RAAF.

DAURA GA WAKILAN RASSA -RAAF.

A jiya Alhamis da dare, da yau safiyar Juma’a 17&18/11/ 2022 Mu’assasar Rasulul A’azam (RAAF) ta kasa ta gabatar da takaitacciyar daura (course) na wakilan rassan ta da ke fadin kasar nan, a cibiyar ta da ke birnin Kano, game da “inganta hanyoyin karantarwa da isar da sako.”

Manyan shehunan malaman wannan Mu’assasa sune suka gabatar da muhimman darussa mabanbanta, sune; Shugaban Mu’assasar kuma wakilin shari’a na Jogaran Musulmai Sayyid Aliyu Al-Khamine’i (D.Z) a Najeriya, Hujjatul Islam Shaikh Muhammad Nura Dass (H), da Babban Sakataren Mu’assasar Shaikh Saleh Sani Zariya (H)& Shugaban bangaren isar da sako Sheikh Bashir Lawal Kano (H).

An kammala daurar lafiya kuma cikin nasara.

Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ci gaba da dafa wa wannan mu’assar game da kokarin ta na yada karantarwa da sakonnin addinin musulunci bisa karantarwa iyalan gidan Manzon Allah (S.A.W.A)

 

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “DAURA GA WAKILAN RASSA NA RAAF.”