September 18, 2021

Dattijo Mai Hikima – Muhimmancin Aikata Alheri

Daga Muhammad Awwal Bauchi


Wata rana wani tsoho mai hikima yana zaune a bakin wani tafki. Kwatsam sai ya ga wata Kuliya (Mage) ta fada cikin wannan tafkin, tana ta kokarin fita don tseratar da kanta daga halaka.

 

Sai dattijon nan ya nufi wajen don ceto ta. Don haka sai ya mika hannunsa don kamo ta. Sai Kuliyar ta yagune shi, sai ya janye hannunsa da sauri yana mai ihu, saboda tsananin zafin da ya ji. Amma ba a jima ba sai ya sake mayar da hannunsa don fitar da Kuliyar, sai ta sake raguninsa. A nan ma ya sake janye hannunsa da saurin saboda zafin da ya ji. Ba a sake jimawa, sai ya sake mai da hannunsa a karo na uku don ceto ta.

 

To akwai wani mutum a kusa da wajen, yana kallon dukkanin abin da ke faruwa tsakanin Dattijon da Kuliyar. Don haka a lokacin da ya ja Dattijon yana kokarin mai da hannunsa a karo na uku, sai ya yi masa tsawa ya ce:

“Ya kai wannan! Ba ka dau darasi a karon farko ba, haka nan a karo na biyu, yanzu kuma ga shi kana kokarin sa hannunka a karo na uku? Kai kan wani irin mutum ne?

Dattijon nan dai bai kula da shi ba, ya ci gaba da kokarinsa na ceto Kuliyar nan. Har daga karshe dai ya sami nasarar ceto ta.

Daga nan sai ya nufi wajen wannan mutumin, ya dafa kafadarsa ya ce masa:

“Ya kai dana!…..Yaguni dai dabi’ar Kuliya ne. So da tausayi kuma suna daga cikin dabi’una. Me ya sa kake so in bar dabi’arta ta yi galaba a kan dabi’ata?

Ya kai dana! Ka yi mu’amala da mutane da dabi’arka ba da dabi’arsu ba. Duk irin munin mu’amalar da suka yi maka a wasu lokuta, kada ka saurari muryoyin da suke kiranka zuwa ga watsi da kyakkyawar siffa da dabi’ar da kake da ita

SHARE:
Makala 0 Replies to “Dattijo Mai Hikima – Muhimmancin Aikata Alheri”