October 23, 2021

‘Daruruwan fursunoni sun tsere yayin harin ‘yan bindiga a kurkukun Oyo

Daga Isah Musa Muhammad


‘Daruruwan fursunonin dake tsare a gidan gyaran hali na Abolongo a jihar Oyo sun tsere a yayin da yan bindiga suka kai hari magarkamar.

Wasu daga mazauna yankin sun shaidawa yan jaridu yadda lamarin ya faru, sun kuma tabbatar da cewa hakan ya faru ne a daren juma’a da misalin karfe 10.

Rahotannin sun nuna cewa mashigar kurkukun an tashe ta da bam, wanda hakan yayi sanadin watsewar masu kula da gidan kurkukun.

Mai magana da yawun hukumar ta gyaran hali a jihar Oyo, Olanrewaju Anjorin ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya bayyana cewa harin ya faru ne yan awanni kadan bayan gwamnatin tarayya ta alakanta masu daukar nauyin Sunday Igboho da masu daukar nauyin kungiyar yan ta’addan Boko Haram.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “‘Daruruwan fursunoni sun tsere yayin harin ‘yan bindiga a kurkukun Oyo”