August 18, 2021

Daren Ashura

Daga Muhammad Awwal Bauchi

Bukatar da Imam Husaini na daga lokacin bayyana kudurinsa na karshe bai kasance da nufin yin tunani a kan al’amarin ba, don ya riga ya gama da wannan tuni yana bisa basira kan al’amarinsa; ya dai so ne wannan daren, wanda shi ne karshen darensa na duniya, ya zama daren da zai raya shi da ibada da addu’o’i; daren sallama ne da wasiyya ga iyali da masoya, domin shi yana sane da abin da ke fuskantarsa gobe, don haka ya yi magana da dan’uwansa da cewa:

 

“Koma gare su, in za ka iya, ka sa su jinkirta mana zuwa gobe. Ka kore mana su zuwa wayewar gari, ko ma samu mu yi salla ga Ubangijinmu a wannan daren mu kuma roke Shi, mu nemi gafara daga gare Shi; domin kuwa Shi Ya san na kasance mai son salla da karatun LittafinSa da yawan addu’a da istigfari(1)”.

 

Dare ya rufa, shiru kake ji, tsuntsaye da kwari duk sun natsu, duk nau’o’in abin halitta sun yi barci face iyalan Muhammadu (s.a.w.a) da mataimakansu, su sun kwana a wannan daren ne tsakanin mai salla da addu’a, sai mai karatun Alkur’ani da mai istigifari; tsakanin mai sallama da da mai yin wasiyya ga iyalinsa, ‘ya’yansa da matansa; suka kasance suna hamhami kamar kudar zuma, suna motsawa suna shirin haduwa da Allah Madaukaki, suna gyaran takubbansu da tanajin masunsu.

 

Sun kwana a wannan daren a matsayin bakin Karbala, tarihi ya kwana yana jiran faruwar babban al’amari da abin da yake tare da shi da safe; ya kwana da shirin rubuta mafi tsatsenin rubutu a rayuwar dan Adam.

 

Husaini yayi sallama da iyalansa da masoyansa, ya ziyarci Imam Sajjad, Sakina, Laila da karamin jikansa al-Bakir (a.s.) da sauran mutan gidansa alhali yana gabatar da wasiyyarsa ta karshe, yana mai mika wuya da kaddara, ya sayar da kansa ga Allah, ya kuduri aniyar shayar da bishiyar shiriya da imani da jininsa da tarin wahalhalunsa.

 

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Daren Ashura”