November 14, 2021

DARASIN HADIN KAN MUSULMI DAGA MAULIDI [2]

Daga mimbarin
Sheikh Saleh Zariya (H)
salehzaria@gmail.com
5/11/2021

Wannan shi ne ci-gaban jawabi dangane da matakan Hadin-Kai…

Hadin-Kai tsakanin Musulmi da Mabiya addinin Kirista masamman: AlKur’ani ya hado hankulan mabiyansa a kan kusanci na musamman tsakaninsu da Kiristoci, Allah Yana cewa: “Kuma lallai za ka samu (daga mutane) mafiya kusantarsu a soyayya ga wadanda suka yi imani su ne wadanda suka ce ‘lallai mu Kirista ne’, wannan kuwa saboda akwai Qissisai (sune limaman Kirista) a cikinsu, kuma hakika su ba sa yin girman-kai. Kuma a duk lokacin da suka ji abin da aka saukar ya zuwa ga Manzo sai ka ga idanuwansu na zubar da hawaye saboda abin da suka sani na gaskiya, suna cewa ya Ubangijinmu mun yi Imani, Ka rubuta mu tare da masu sheda” (al-Ma’idah/82-83).

Daga cikinsu kuwa duk wadanda suka bi hanyar zalunci da keta haddin Musulmi, su ma sai mu’amala da su ta zama tamkar ta wadanda ambatonsu ya gabata a karshen kasha na [1], mai magana a kan Hadin-Kai tsakanin mabiya addinan sama gaba daya.
[e] Hadin-Kai tsakanin Shi’a da Sunna: Makiya Musulmi sun dade suna rabewa da sabanin Shi’a da Ahlussuna don cimma manufofinsu. Wannan ya rika faruwa ne saboda yunkure yunkuren aje wani bangare a gefe, da yada karairayi da haifar da nisantar-juna a tsakanin wadannan shakikai biyu, wanda wasu mahukuntan Musulmi suka rika yi tare da goyon bayan wasu gurbatattun malaman Musulmi; wanda hakan ne ya rika samar da gibin da makiya dukkan bangarorin biyu suke rika amfana da shi wajen fadada tazara tsakanin su. A yau ma, babu sabanin da makiya suka fi nacewa a kansa kamar sabanin Shi’a da Ahlussunna. Wannan ya sa mukhlisan malaman bangarorin biyu suka mike tsaye wajen fayyace gaskiyar al’amari da kara kusato juna. Bayanin matsayan manyan cibiyoyin nan biyu na Shi’a da Ahlussunna, wadanda bayaninsu ya gabata, ya wadatar da ya bayar da sura a kan wannan kokari.

Abin takaici ne ganin yadda a baya bayan nan, wadancan makiya suka iya yin kutse ta hanyar yaudara wajen kokarin raba zumuncin da son Manzon Allah da Ahlinsa ya haifar a tsakanin wasu mabiya darikun Sufaye da ’yan Shi’a, inda muke ganin wani hankoro na tayar da hassasiyoyi da mas’alolin sabani tsakanin bangrorin biyu.

Babu shakka akwai shedanun da suke boyewa a bayan fage suna daukar nauyin wannan hankoro, wanda ba za su yi nasara ba da yardar Allah. Ga karnukan-farautar da ake turowaa don wannan hankoro nake cewa: ku tabbatar da cewa babu nasara a tare da yunkure-yunkuren ku. Ga ’yan Shi’an da suke cikin irin wannan katobara nake cewa: da ban takaici ga wanda Imamansa suka ba shi kyawawan misalsali na rayuwa tare da wadanda suke da sabanin fahimtar addini da su, amma ya fada tarkon makiya cikin sauki. Kiran mu ga ’yan Shi’a shi ne cewa mu zama kyawawan wakilan tafarkin Ahlul-Bait (AS), kamar yadda suka hore mu a cikin abin da ya zo ta hanyar Sulaiman bin Mihran (Bihar al-Anwar, Juz’i na 68, shafi na 310), ya ce: “Na shiga wajen Imam Imam al-Sadiq (AS) sai na iske shi tare da wasu ’yan Shi’a, sai na ji shi yana cewa: “Ya ku jama’ar Shi’a! ku zame mana kwalliya, kar ku zame mana kazanta. Ku fadi magana mai kyau ga mutane; ku kiyaye harshenku, kuma ku kame su daga abin da ya karu na daga mummunar magana”. Tasa shugabannin al’umma a gaba da wadanda suke ganin girma da mutuncinsu kuwa ya sabawa “kiyaye harshe” da zama “kwalliya” ga Ahlul-Bait. Alhali su suke fada (kamar yadda ya zo a cikin Nahjul-Balagha) cewa: “Ina yi muku kyamar ku zama masu zage-zage; da dai za ku siffanta ayyukansu, kuma ku ambaci halayensu, da haka ya fi muku daidai a magana, kuma da (ya fi) isarwa ga uzuri; kuma a madadin zaginsu (da kun) rika cewa: ‘Ya Allah Ka kare jinanan mu da jinainansu, Ka kuma kyautata tsakanin mu da su, Kuma Ka shiryar da su daga batan da suke kai, ta yadda wanda ya jahilci gaskiya zai santa, kuma wanda ke furuci da zalunci da kiyayya ya kame daga gare su” (huduba ta 206). Wannan shi ke layin karantarwar Marji’an mu daga fahimtar nassosin da suka fito ta hanyarsu (AS). Amma yawace-yawace da yanko nassosi “out of context”, wannan ba karantarwasu ba ne, kuma ba ya taimakon tafarkinsu mai albarka, masamman a duniyar yau, kuma masamman a kasar nan.

Ma’anar wannan Hadin-Kai a nan shi ne kiyaye zamantakewar mu da kawar da kai daga abin da zai iya kawowa al’umma tsaiko kamar yadda suka tabbatar a rayuwarsu (AS). Ya zo a sharhin Nahjul-Balaga na Ibin Abil-Hadid, juz’i na 6, shafi 166, da littafin Hayatu Amiril Mu’uminin an Lisanihi, na Muhammad Muhammadiya, juz’i na 3, shafi na 251, daga hudubar Imam Ali (AS) cewa: “Hakika ku sani cewa ni nafi cancantar sa (Khalifanci) a kan wanina; kuma wallahi zan hakure a kan duk abin da lamarin Musulmi zai kubuta daga gare shi, (matukar) zalunci a kansa zai takaita da ni kadai ne, bisa kamun kafa a kan ladan haka da falalarsa, da gujewa abin da kuke rige-rigensa na daga kyale-kyalensa da kwalliyarsa (kamar yadda kuke kallon khalifanci).

Sai dai fa a nan babu sassauci a kan zama daram a kan akida da wilaya ga Alhlu-Baiti (AS). Kamar haka, cakuda lamurran zamantakewar lumana da sauran Musulmi da al’murran da suka jimanci mazhaba kuskure ne babba.
[f] Hadin-Kai tsakanin Shi’a da Shi’a: A nan abubuwa uku nake kira kamar haka:
Kiyaye ’ya’uwantakar akida da dora turbar na-baya da mu a kan asasan sharuddan adalci da kiyaye hakkoki. Wannan yana daga abin da duk dan Shi’a ya sani a tsarin karantarwar tafarkin su (AS).
Sanin yadda za mu rika fuskantar munanawa da kurakuran mu bisa afuwa da hakuri: “Kuma kyautatawa ba ta daidaituwa, da munanawa; ka tunkude cutarwa da abin da yake mafi kyau, (da haka) sai ka ga wanda a tsakanin ka da shi akwai wata kiyayya da zama kamar masoyi ne majibinci. Babu wanda ke daukar wannan sai wadanda suka yi hakuri, kuma babu mai daukar wannan sai mai babban rabo” (Fussilat/34-35). A gaba ayar ta bayyana cewa fizguwa zuwa rarraba yana iya kasancewa daga fizgar shedanu (daga mutane da aljanu) ne: “Kuma idan wata fizga ta fizge ka daga shaidan, to ka nemi tsari daga Allah, lallai Shi (Allah) Shi ne Mai ji Masani” (Fussilat/36).

Tabbatar da mutunta hakkoki da gujewa tauye su ko kwace mallakokin junan mu da amanonin dake karkashin kowa, da gujewa cuta da cutarwa da ta’addanci a kan haka. A lokacin da wani dalili ya haifar da wannan abin takaici, to Allah Ya yi umarni ne da a taimaki wanda aka zalunta a tsakanin masu sabani: “Idan bangarori biyu na muminai suka sami tashin-tashina a tsakaninsu, to ku sulhunta tsakaninsu, idan kuwa daya ta zalunci daya, to ku yi taron-dangi a kan wadda ta yi zalunci har ta koma zuwa ga horon Allah; idan ta dawo, to ku sulhunta a tsakaninsu da adalci kuma ku daidaita, lallai Allah Yana son masu daidaitawa, Muminai ’yan’uwan juna ne, don haka ku sulhunta tsakanin ’yan’uwanku, ku ji tsoron Allah don ku sami rahama” (al-Hujurat/9-10).
Duk wani kira a kan danne hakkin wani da mika shi ga wani bangare yayin sabani a kan hakkoki, lallai hakan kokarin danne mai hakki ne kawai, wanda hakan ba zai karbu ba.

Hangen Rasulul A’azam (RAAF) a Kan Hadin-Kai
An gina gidauniyar Rasulul-A’azam (RAAF) ne a kan assasa Shi’anci ta dukkan fuskoki, da kyautata sunansa mai albarka wanda yake fuskantar gurbatawa da batawa daga sassa dabam daban, gina tunanin ’yan Shi’a a kan abin da ya shafi maslaharsu ta lahira da duniya, tare da kokarin tabbatuwar karin kusantar juna tsakanin mabiya Ahlul-Bait (AS) a kasar nan! A kan haka shugabannin kungiyar suka rika kamewa daga furtawa ko aikata duk abin da suka fahimci zai batawa wani bangare, kai! hatta bude cibiyoyin karantarwa (wanda yake daga jigogin ayyukanta) sai da ta rika yin yakanarsa a duk inda ake da samuwar wani malamin Shi’a ko cibiyar wata kungiyar Shi’a, koda kuwa ba ya yin irin ayyukan da take ganin shi ya kamata a gabatar ko aikata abin da take ganin cutarwa ne ga akidar Shi’a. A kan haka ne shugabanninta suka rika bibiyar ’yan Gwagwarmaya ta hanyar shugabanninsu, masamman babban jagorancinsu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, har zuwa sauran masu taka mahimmiyar rawa a fagen kasar nan!! Da wannan mataki ta cirata tunaninta a kan Hadin-Kai, ta fito baro-baro ta bayyana cewa ya wajaba kowa ya kare sinadarin “Shi’aci Zalla” a matsayin abin da ya hada mu gaba daya, da cewa a kiyayi shigar da duk wasu harkoki a matsayin Shi’anci matukar ba ainihin Shi’ancin ba ne. Haka nan ta bukaci kiyaye kwashe-kafar sauran mabiya Shi’anci da kokarin lankaya musu abin da ba su yi imani da shi ba; da kiyaye mutuncin Shi’anci da kariya ga karantarwarsa a fagen Nijeriya; da cewa a dora dukkan mabiya Shi’a kan turbar Marja’iyya da shiryarwar cibiyoyin ilimin Shi’a na Qum da Najaf; suke cewa a kira kowane abu da sunansa na yanka, ta hanyar kiran kowane lamari da ainihin sunansa, da bude kofofin al-Amru bil-Ma’arufi wal-Nahyu anil-Munkari a tsakanin mabiya Shi’a a kasar nan a kan asasin kiyaye sharuddansu. Amma, abin takaici, wannan kira bai samu karbuwa a wajen shugabannin wasu bangarori masu tasiri a kasar da wasu mabiyansu ba, yayin da suka dage a kan wajabcin a baje RAAF a karkashin masu tarin jama’a da sauran irin haka; wanda RAAF kuma ta ki yarda da haka. A sakamakon haka ne, bayan shekaru kusan goma da irin wannan ja-in-ja, gidaunyar RAAF ta dauki kudurin sanar da cikakiyyar ’yancinta na zartar da abubuwan da ta yi ammana da su a kan aikin Shi’anci a fagen Nijeriya gaba daya; a shekara ta 2010 sai kungiyar ta gabatar da kanta ga al’ummar Nijeriya, ta dauri aniyar gabatar da abubuwan da ta yi imani da su da wadanda ba ta yi imani da su ba ga ‘yan Shi’a gaba daya, ba tare da tsoron zargin mai zargi ko cece-kucen mai cece-kuce ba. Har zuwa yanzu din nan haka take tafiya.
A kan haka RAAF ta tsaya a kan matsayinta dangane da cibiyarta da wani sashen ’yan Shi’a -wadanda gudunmawarsu ga gininta yake kasa da kashi talatin bisa dari amma – suka kwace shi a Gombe, alhali wadanda suke korafi a kan haka su suka sarrafa sama da kashi saba’in bisa dari – banda cewa daga cikinsu ne suka sarrafa dukkan lokutansu da tunanisu don tabbatar da wannan gini – amma wadancan ’yan tsiraru suka balle makullan ginin suka karbe shi, a yanzu ’yan kungiyar RAAF ba sa tasarrufi da ginin, kuma ba su mallaki komai ba sai tunatarwa a kan cewa wannan wuri fa kwatacce ne. A ganin RAAF, duk wani kokari na kawar da kai da hakkinta a kan wannan gini, ko da me aka kira haka, ba ya layin Hadin-Kai, idan ma ba a dauke shi a tsagwaron zalunci ba.
Haka nan RAAF ta tsaya a gaban sababbin matakan dake faruwa a duniyar Shi’a na kafirta wasu Sahabbai da zaginsu, da zargin Ummul-Mu’minina A’isha da alfasha (wal’iyazu bilLahi), da cusa wasu abubuwan kyama a cikin ayyukan raya Sha’a’ir na Imam Hussain (AS). Dalilinta a kan haka shi ne la’akari da cewa asalin karantarwar Ahlul-Bait (AS), kamar yadda galibin Marji’an Shi’a suka bayyana a fatawoyinsu da karantarwarsu, sun yi hannun-riga da irin wadannan zantuka da ayyuka. Akwai Marji’an da ta sababinsu galibin ’yan Shi’ar kasar nan suka fahimci Shi’anci kuma da su ake taqlidi, don haka a kan turbar irin wadannan Marji’ai RAAF take gina kiraye-kirayenta.
Allah Ya hada mu a kan gaskiya da adalci.

SHARE:
Tsokaci 0 Replies to “DARASIN HADIN KAN MUSULMI DAGA MAULIDI [2]”