November 10, 2021

DARASIN HADIN KAN MUSULMI DAGA MAULIDI [1]

Daga Mimbarin Sheikh Saleh Zariya (H)
salehzaria@gmail.com
5/11/2021


[Allah] Shi ne Wanda ya aiko ManzonSa da shiriya da addini na gaskiya don ya daukaka shi a kan addinai dukkansu, ko da Mushirikai basu so ba (al-Saffi/9).
Daga ayar da ta gabata, ana iya fitar da mahimman sinadarori guda uku da masu Maulidi ke tattauna su: [1] Manzon Rahama (SAWA); [2] sakon da ya zo da shi daga Allah; da [3] al’ummarsa. Na farko ya kebanci darasi a kan duk abin da ya shafi Manzon Allah (mai tsira da aminci); tun daga asalin haskensa (wanda shi ne farkon abin da Allah Madaukaki Ya halitta), zuwa tsatsonsa mai albarka, haihuwarsa, girmansa, halayensa, aurensa, saukar Wahayin Allah zuwa gare shi, gwagwarmayarsa a Makka, hijirarsa zuwa Madina, Jihadodinsa, da wasun wadannan na daga lamurran dake walwalin sheki game da shi, wadanda su ne jigogin abubuwan da suke haifar da Maulidi da bunkasarsa. Na biyu kuwa ya kebanci sakonsa na Musulunci ne, AlKur’ani mai girma, Shari’a mai tsarki da makomar wadannan bayansa, wadanda su ne ainihin abubuwan da ya yi aiki tukuru don su, ya kuma hakurewa bakin-ciki da bacin-rai da cutarwa a sabili da tabbatar da su.

Na uku kuma su ne al’ummarsa, wadda ya yi aiki tukuru wajen gina ta, ya yi matukar aiki don ganin ta kafu da gindinta, da ajiyeta a matsayin wadda za ta dauki amanar sakonsa, a matsayinta na danshin idonsa kuma sakamakon kokarinsa. Don haka hadin-kan ta ya zama jigo a tafiyar ta na sauke nauyin da ya dora mata.

Na ukun karshen nan, wato al’ummarsa, shi ne maudu’in wannan makala, ta hanyar kallon jigo daga lamarin da shi ne zai ba ta damar sauke nauyin da ya doru a kanta, wanda ba tare da shi ba za ta cutar da kanta ta hanyar zama mai ha’intar amanar Allah da ManzonSa, da kawar da kai daga babban abin da ya farlanta mata; wato

HADIN-KAN MUSULMI.

Ma’anar Hadin-Kai
Da hakdin-Kai, wannan makala ba ta nufin “Hadin-Baki” ko “Hadin-Guiwa” a kan rashin gaskiya da cin amana . Manufar hakika na hadin-kan Musulmi shi ne “taimakeniya a kan gaskiya da tsoron Allah” kamar yadda Allah Ta’ala Ya umarci Musulmi da su aikata haka, a cikin fadinSa: “Kuma ku yi taimakekeniya a bisa abin kirki da tsoron Allah, kuma ka da ku yi taimakekeniya a kan sabo da keta haddi” (al-Ma’dah/2). Hadin-Kai ya ginu ne a kan hangen cewa: [a] Musulmi al’umma daya ce mai Ubangiji daya, mai manufa guda da akida da ayyukan ibadu iri daya. [b] Wajabcin fahimtar makamar juna, don bukasar ilimi da fahimta [c] Hadin-Kai ne hanya makadaiciya dake iya baiwa al’ummar Musulmi kariya daga kutunguilolin makiya da ’yan tsirku da munafukai.

Nassosin Musulunci Hadin-Kai
Musulunci ne ya umarci Musulmi da su tabbatar da hadin-kai a tsakaninsu, kuma su gujewa rarrabuwar-kai, nesanta da kyamar juna, samar da taimakekeniya a tsakaninsu a bisa asasin alheri da gujewa sharrace-sharrace. Ya tabbatar da haka ta hanyoyinsa na karantarwa kamar:
Na Daya: AlKurani – a cikin ayoyinsa na horo da hani da misalsalinsu. Allah yana cewa: “Ku bi Allah da ManzonSa; kuma kar ku yi jayayya har ku raunana (ta yadda) karfin ku zai gushe; ku yi hakuri, lallai Allah Yana tare da masu hakuri” (al-Anfali/46). Ya kuma ce: “Kuma ku yi riko da igiyar Allah gaba daya kada ku rarraba. Ku tuna da ni’imar Allah a kanku a lokacin da kua kasance makiya juna, sai [Allah] Ya dasa soyayya a cikin zukatanku, sai kuka wayi gari, bisa ni’imarSa, ’yan’uwan juna. Kuma a baya kun kasance a gabar wuta, sai ya kubutar daga barinta; da haka Allah Yake bayyana muku ayoyinSa ko kwa shiriya” (aali-Imran/103). Kuma ya nuna al’ummar Musulmi a matsayin al’umma daya, da cewarsa: “Lallai wannan al’umma ta ku al’umma ce guda daya kuma Ni ne Ubangijin ku don haka ku bauta min” (al-Anbiya’i/92); da cewa: “Lallai wannan al’umma ta ku al’umma ce guda daya kuma Ni ne Ubangijin ku don haka ku ji tsoro Na” (al-Mu’minun/52). Kamar yadda Sheikh Abubakar Gumi yake fada, a karin bayanin tarjamar wannan aya (a shafi na 496 na Tarjamarsa ga ma’anonin AlKura’ni zuwa harshen Hausa) cewa: “al’ummar Musulmi duka guda ce koda yake Annabawansu sun zo dabam-dabam, a cikin lokuta masu nisa a tsakaninsu da harsuna dabam-dabam, domin duk akidarsu guda ce a kan Ubangiji guda ne. Sa’an nan daga baya wadanan suka fita daga wannan akidar suka rarrabu kungiya-kungiya”.
Na Biyu: Sunnah – Ta kunshi zantuka da ayyuka da ikirarorin Manzomu mai daraja (SAWA) – a fahimtar ’yan Shi’a haka ma zantuka da ayyuka da ikirarorin Ma’asumai daga Ahlul-Bait (AS). Duk sun kunshi umarni da hadin-kai da hani da rarraba (ba su yi hani da sabanin fahimta ba). Kamar fadinsa (SAWA), wanda ya zo a cikin ingantaccen hadisi, mai cewa: “Jinainan Musulmi suna daidaita (a haddodi da kisasi). Wadanda ke biye musu kuma -na daga kafiran amana – suna kasansu. Kuma su -Musulmi- hannu daya ne a kan wadanda ba su ba” (duba al-Musannaf na bin Ibin Abi Shaibah, juz’i na 6, shafi na 441, Littafin Diyyoyi, hadisi na 3913). Haka nan ya zo a cikin Sahih Muslim, hadisin Nu’uman bin Bashir, daga Manzo (SAWA) ya ce: “Misalin Muminai a kaunaceceniyarsu da tausayin junansu da jinkan junansu kamar jiki daya ne, idan gaba daya ta yi rashin lafiya sai sauran jiki ya amsa da rashin bacci da zazzabi” (duba Sahih Muslim, juz’i na 6, shafi na 565, hadisi na 2494 a littafin al-Birru was-Silah). A ruwayar Ahmad bin Hambali cewa ya yi: “Musulmi kamar mutum guda ne, idan idaniyarsa ta yi ciwo sai dukkansa ya koka, idan kansa ya yi ciwo sai dukkansa ya koka” (Ahmad ne ya ruwaito a juz’i na 4, shafi na 260). A bisa wannan haske ake fahimtar “Hada ‘Yan’uwantaka tsakanin Muhajirai da Ansar” bayan hijirar Manzo (SAWA) daga Makka zuwa Madina.
Na Uku: Zantuka da Ayyukan Nagartattu daga Malamai: A matsayinsu na magada Annabawa, wasu nagartattu daga malaman al’ummar nan sun sauke wannan nauyi na aikatawa da kira zuwa ga hadin-kan Musulmi gaba daya, masamman a lokacin da kutunguilar makiya addinin Musulunci da yunkurinsu na haifar da rarraba-kan Musulmi suka bayyana gare su baro-baro. Haka za mu gani a yukurin mutane irin su Sheikh Jamaluddin al-Afghani, Sheikh Muhammadu Abduh, Ayatollahi Sayyid Sharfuddin al-Musawi, Sheikh Salim al-Bishir, Ayatollahi Sayyid sl-Burjurdi, Imam Musa al-Sadr, Imam al-Khumaini, Sayyid al-Qa’id al-Khamina’i, Sayyid al-Sistani, Allamah Sayyid Fadlullah. Haka manyan cibiyoyin Shi’a (massaman Hauzar Qom), da na Ahlus-Sunna (masamman Jami’ar al-Azhar) sun misalta haka ayyuka da zantukan shugabanninsu da malamansu. Misalai daga haka sun kunshi fatawoyin da malaman Shi’a suke fitarwa na haramcin furtawa ko aikata duk abin da zai haifar da rarraba kan Musulmi. Haka matakin shugaban Jami’ar Azhar da Shehunnan ta masu tabbatar da cewa Shi’a (Imamiyya da Zaidiyya da Isma’iliiya) da Ibadhiyya suna daga Mazahabobin Musulunci kamar na Ahlussunna guda hudu, wadanda za a iya bautar Allah ta bin kowacce daga cikinsu. Ga misalin bayanin Shekhul-Azhar mai ci, Sheikh Ahmad Tayyib, cewa “Shi’a da Sunnah fika-fikai biyu ne na wannan al’umma, wadanda da su take iya tashi”.

Matakan Hadin-Kai
Masu rajin Hadin-Han Musulmi a duniya ba sa takaita hangensu da bangare daya na hadin-kai. A lokacin da suke kiraye kirayen Hadin-Kai, ana fahimtar kiransu da dukkan fuskoki; kamar:
[a] Hadin-Kai tsakanin Muslmi kansu: kamar yadda nassosin addini da aka gabatar suka tabbatar. [b] Hadin-kai tsakanin ’yan Adam gaba daya: kamar yadda ya zo cikin AlKur’ani cewa: “Ya ku mutane hakika mun halicce ku daga namiji da mace, sannan muka sanya ku dangogi da kabilu don ku san juna, lallai mafificin ku daraja a wajen Allah shi ne wanda ya fi ku takawa; lallai Allah Masani ne kuma Mai bayar da labari” (al-Hujraat/13). Ga irin fadin Imam Ali (AS), wanda ya zo a cikin nassin ahdinsa ga Malik al-Ashtar, lokacin da ya nada shi gwamnansa a Masar, kamar yadda ya zo a sashin wasiku na cikin Nahjul-Balagha cewa: “…domin kuwa su (mutane) iri biyu ne: ko dai dan’uwanka a addini ko tamkarka a halitta..” (Allama al-Majlisi, Bihar al-Anwar, juz’i na 33, shafi na 660).
A nan tilas a ambaci cewa dole Hadin-Kan ’yan Adam ya zama a kan asasin abubuwan da suka hada zamantakewarsu da gujewa abubuwan da ka iya kawo rikice-rikice da gurbacewar lumana a tsakaninsu.

[c] Hadin-Kai Tsakanin mabiya addinan Sama gaba daya: Saboda AlKur’ani ya ambaci samuwar sabani a tsakninsu da cewa: “(Da farko) mutane sun kasance abu daya ne; sai Allah Ya aka da Annabawa (zuwa gare su) a matsayin masu albishir da gargadi, ya kuma saukar da Littafi da gaskiya tare da su, don su yi hukunci a tsakanin mutane kan abubuwan da suka saba a kai; kuma babu wanda ya saba a kansa sai wadanda aka zowa da shi, bayan bayanai (hujjoji) sun isa gare su, bisa zalunci a tsakaninsu, sai Allah Ya shiryar da wadanda suka yi Imani a kan abin da suka sassaba a cikinsa na daga gaskiya bisa izininSa; Allah (kuwa) yana shiryar da wanda Ya so zuwa tafarki madaidaici” (al-Baqara/213).

Sai ya bayar da samfurin zamantakewa da irin wadannan mutane da cewa ya ginu ne a kan adalci da girmamawa tare da rashin tauye hakkokin juna: “Allah ba Ya hanin ku daga wadanda ba su yake ku ba a kan addini, kuma ba su fitar ku da daga gidajenku ba, a kan ku kyautata musu kuma ku yi musu adalci; lallai Allah Yana son masu adalci. Ya hane ku ne kawai a kan wadanda suka yake ku a kan addini, kuma (ko) suka fitar da ku daga gidajen ku, kuma (ko) suka yi taron-dangi a kan fitar da ku, da kar ku jibince su; wanda kuwa ya jibince su (irin) wadannan su ne azzalumai” (al-Mumtahanah/8-9).

Amma idan wasu suka tsaya a kan sai sun zalunci Musulmi a kan hakkokinsu kuma duk hanyoyin lalama suka ki aiki, to a nan Allah Ya umarci Musulmi da su kare kansu: “An yi izini ga wadanda ake yakarsu da cewa lallai an zalunce su, kuma lallai Allah Mai iko ne a kan taimakonsu; wadanda aka fitar da su daga gidajensu ba da wani hakki ba, illa don sun ce ‘Ubangijinmu Allah ne’. Kuma ba domin tunkudewar Allah ga mutane ta hanyar kariyar mutane sashensu ga sashe ba da an rushe matattaran malaman Ahlul-Kitabi da Majami’un Kirista da wuraren bautar Yahudawa da Masallatai, wadanda ake ambaton Allah da yawa a cikinsu. Hakika Allah Yana taimakon wanda yake taimakonSa, kuma hakika Allah Mai karfi ne Mabuwayi” (al-Hajj/39-40).
Akwai Dorawa a nan Gaba insha’allah.

SHARE:
Tsokaci 0 Replies to “DARASIN HADIN KAN MUSULMI DAGA MAULIDI [1]”