May 26, 2023

DARASI DAGA ƘISSAR WASU YAHUDAWA

 

Daga Malam Muhammad Bakir Ibrahim

KYAUTATA HARSHE
An rawaito cewa wata rana wani Bayahude ya shigo wajen Manzon Allah (s) sai ya ce masa: “Assamu Alaikum” (Wato bala’i a kanku), na biyu da na uku ma suka shigo duk haka nan dai. Sai Annabi (s) ya amsa musu iri ɗaya da cewa: “Alaikum” kaɗai… Nana A’isha (r) tana wajen, sai ta fusata, take ta ce da su: “Bala’i a kanku dai! fishi da tsinuwa ya ku taron Yahudawa, ƴan’uwan birai da aladu”

Sai Manzon Allah (s) ya ce da ita: “Ya A’isha! Haƙiƙa da ace alfasha abu ne da ake iya gani, to da zai kasance mummuna ne. Haƙiƙa tausasawa da za a auna shi da wani abu, to da sai ya rinjaye wannan abun…”

Sai ta ce: “Ya Rasulallahi shin ba ka ji zancensu (na fatan bala’i a kanmu) ba ne?” ya ce: “Ƙwarai na ji! Shin ba ki ji yadda na amsa musu ba ne? Cewa na yi: “A kanku (na yi shiru iya nan)” (Al-Kafi: 2/648).

____________
D A R A S I !
Ɗaya daga darussan da za mu iya tsinta a nan shi ne KYAUTATA HARSHE da KIYAYE SHI DAGA MUNANAN KALAMAI. Har su uku waɗannan Yahudawa suka rinƙa yi wa Annabin Allah fatan bala’i, amma me? Hakan be sanya shi ya fusata ya munana harshe ko da irin nasu ba, ballantana fiye da na su…

Baka ji ba? Nana A’isha (r) ta fusata ta yi musu martani har da ƙari saboda zafin abinda suka yi. Amma nan Rahmatan Lil-Alamina (s) ba kawai shiru ne be yi ba, tsawatarwa yayi, ya kwaɗaitar ne ma zuwa ga tausasa harshe ga wanda ya kausasa mana ko da kuwa muna da saɓani da shi. Domin ko ba komai akwai lada a cikin hakan!
Allah ta’ala ya kiyaye mana harsunanmu da zamewa!

SHARE:
Makala 0 Replies to “DARASI DAGA ƘISSAR WASU YAHUDAWA”