Ahlul Baiti

Jaridar Isar da Sakon Jikokin Manzon Allah (S.A.W)

June 16, 2023

DARASI DAGA ƘISSAR WANI MUSULMI.

 

ILLAR TSAURARAWA A SHA’ANIN ADDINI.

Daga Malam Bakir Ibrahim Saminaka.

An rawaito cewa” Wani mutum ne Musulmi yake da maƙwafci wanda ba Musulmi ba; Kuma suna tattaunawa a kan musulunci wasu lokutan… Har wannan mutumin ya musulunta saboda kyawun Muslunci da yake ji…
Kwatsam! Washegari da asussuba wannan sabon Musulmi ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofrsa, sai ya tambaya wa ke ƙwanƙwasa ƙofa?
Musulmi: Ni ne wane, maƙwafcinka.
Mutumi: Me ya kawo ka a wannan lokacin?
Musulmi: Ka yi maza-maza ka yi alwala ka sa kaya ka fito mu tafi Masallaci mu yi salla.

Haka dai wannan mutumi (da ya musulunta) ya yi alwala ya fito suka tafi, karon sa na farko ke nan da ya fara zuwa Masallaci… Nan fa suka yi ta salloli har aka zo suka sallaci sallar Asuba, suka yi ta addu’o’i har gari ya waye. Nan fa wannan mutumi ya yi nufin ya tashi ya tafi gida.
Sai Musulmi ya ce masa: Ina zuwa?
Mutumi: So nake in koma gida, ai mun gama sallar asuba ɗin kuma…

Sai wannan Musulmi ya ce: “Saurin me kake yi ne haka? Mu cigaba zuwa ɗan an jima. Mutumi ya haƙura ya zauna… Can ya yunƙura zai tafi, Musulmi ya ce “Mu ɗan yi karatun Alƙur’ani mana zuwa rana ta ɗan ɗaga, nan ya karanto mishi falalar azumi ya ce “mu ɗaura niyya ma mu ɗau azumi (na nafila)…” Haka nan aka yita tafiya…

Da Azahar ta gabato; Musulmi ya ce: “Ka yi haƙuri kaɗan, saura ƙiris a yi Azahar…” An yi azahar ya sake cewa “Ka daure dai, ai La’asar ma ta kusa kuma an fi son mutum ya yi ta a kan lokacinta”
An yi sallar La’asar ya sake cewa “Yamma ma ta kusa fa, ka jira har a yi Magariba kawai…”
Haka nan dai wannan mutumi ya daure, ana yin Magariba kuwa ya ce “Ai dai yanzu babu wata farilla da ta rage mana sai ta Isaha’i ko?” sai ya miƙe ya yi ta ya fice zuwa gida…

Kuma dai! Washegari da asussuba wannan Musulmi ya sake dawo masa, wai su tafi Masallaci… Mutumi kuwa ya ce “Ni kam wannan Addinin naka ya ishe ni, ka je ka nemi wani wanda ya fi ni ƙwazo, wanda zai iya ƙarar da lokacin(wunin)sa a masallaci. Domin Ni mutum ne mare ƙarfi, kuma ina da iyalai, dolena in fita yin aiki don neman arziƙi!”
(Ƙisasul-Abrār:45)

___________
D A R A S I !
Ke nan dai wannan Musulmi shi ya yi sanadin Shigar wancan mutumin Musulunci, haka nan kuma shi ne dai sanadin fitarsa… Ta yaya? Ta yadda ya tsawwala masa, har ya kai ga ya ƙure haƙuri da juriyarsa. Al-Imamus Sadiƙ (a) ya ce: Su mutane suna da dammaki da kuma ikon da ƙabillar yin abu daban-daban ne, don haka ku yi mu’amala da kowanne a gwargwadonsa…

Ya ce “Ku ɗauki wannan a matsayin darasin kada ku tsaurara wa mutane”
“…Imamancinmu yana tsayuwa ne a bisa tausasawa da sauƙaƙawa, da taƙiyya da kuma kyakkyawar cuɗanya. Don haka ku kwaɗaitar da mutane zuwa ga Addininku da abinda kuke ciki (na sauƙaƙawa)”
(A duba masadarin da ya gabata).

SHARE:
Makala One Reply to “DARASI DAGA ƘISSAR WANI MUSULMI.”
Ahlul Baiti
Ahlul Baiti

COMMENTS

One comment on “DARASI DAGA ƘISSAR WANI MUSULMI.

    Author’s gravatar

    MashAllah hakika munji Dadi da samun wannan jaridar,
    AllAh ya taimakeku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *