November 23, 2023

​Daraktan Makabartar Sojojin Isra’ila: “Mun Binne Sojoji 50 Da Aka Kashe A Gaza Cikin Sa’o’i 48

 

Daraktan makabartar sojoji ta Mount Herzl ya bayyana dimbin sojojin Isra’ila da aka binne sakamakon yakin da suke yi a zirin Gaza, inda aka binne sojoji 50 cikin sa’o’i 48.

David Oren Baruch, daraktan makabartar sojoji ta Mount Herzl, ya ce: “Yanzu muna cikin wani lokaci da a kowace sa’a ana yin jana’izar soja da aka kashe.

Ya an bukaci an gina adadi mai yawa na kaburbura, a cikin makabartar Mount Herzl ne kawai muka binne sojoji 50 cikin sa’o’i 48.”

Sannan kuma ba a bayyana sunayen sojojin da suka mutu ba, har sai rundunar sojin ta bayar da damar yin hakan.

Ya yanzu dai rundunar sojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta sanar da sunaye 380 ne kawai a shafinta na yanar gizo, tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

 

©V.O.H

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “​Daraktan Makabartar Sojojin Isra’ila: “Mun Binne Sojoji 50 Da Aka Kashe A Gaza Cikin Sa’o’i 48”