August 7, 2021

Dan Wasan Gaban Nigeriya Ya Samu Tayi Daga Real Mallorca

Daga Baba Abdulƙadir

 

Dan wasan gaba na Najeriya Simeon Simy Nwankwo na iya komawa kasar Spain bayan Real Mallorca ta yi tayin yuro miliyan 1.8 Kuma ana Saran kungiyar zata iya kashe yuro miliyan 3.5 wajen daukar dan wasan a cewar wasu Rahotanni.

 

Kungiyoyin Italiya irinsu Sampdoria, Genoa, Lazio, da Salernitana, an ruwaito cewa suna  zawarcin Simy, yayin da Tottenham Hotspur daga gasar Firimiyar Ingila ke son daukar dan wasan gaban Crotone din Wanda tuni kungiyar ta fada ajin matasa na kasar Italiya Seria B.

 

Duk da ya ke Real Mallorca ta mamaye sauran masu sha’awar daukar Simy tare da tayin kusan Yuro miliyan hudu, a cewar Diario de Mallorca.

 

Crotone ta kashe Yuri dubu 850,000 kawai wajen siyan dan wasan gaba na Super Eagles a 2016 daga Portimonense ta kasar Portugal. Amma bayan kyakkyawan kakar wasan sa ta 2020/21 inda ya zura kwallaye 20 a Serie A kuma ya zama babban ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Crotone, tsohon dan wasan Gil Vicente wanda a yanzu an bayyana darajar sa akan Yuro miliyan 8.

 

Simy mai shekara 29,  yana da ragowar kwantiragin da zai kare a shekara mai zuwa, hakan ka’iya tilasta kungiyar ta Sallamar da Shi a wannan kakar saboda Kar ta rasa dan wasan a kyauta a karshen kakar wasa me zuwa.

 

SHARE:
Labarin Wasanni 0 Replies to “Dan Wasan Gaban Nigeriya Ya Samu Tayi Daga Real Mallorca”