April 2, 2024

Dan shugaban kasar Uganda ya sha alwashin murkushe masu cin hanci da rashawa

Dan shugaban kasar Uganda ya sha alwashin murkushe masu cin hanci da rashawa bayan ya karbi ragamar mulkin soja

Dan shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa a cikin rundunar soji bayan ya karbi mukamin babban kwamandan rundunar, matakin da ake kyautata zaton zai kara saurin hawansa ya gaji mahaifinsa.

Museveni ya nada dansa Muhoozi Kainerugaba mai shekaru 49 a matsayin sabon babban hafsan hafsoshin tsaron kasar ta gabashin Afirka a makon jiya.

A wani bikin mika mulki a hukumance a ranar Alhamis, Kainerugaba “ya sha alwashin inganta jin dadin sojoji ta hanyar yaki da muggan laifuka da almubazzaranci da dukiyar kasa,” a cewar wata sanarwa da rundunar ta fitar.

#Uganda

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Dan shugaban kasar Uganda ya sha alwashin murkushe masu cin hanci da rashawa”