February 4, 2024

Dan Majalisa Ya Roki Yan Najeriya a Bawa Tinubu Shekara Biyu Ya Gyara Tattalin Arzikin kasar

Shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kwastam, Leke Joseph Abejide, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da jure wa radadin tsadar rayuwa, yana mai cewa manufofin tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa za su magance matsalar nan gaba kadan.
Dan majalisar ya yi jawabi ne a Kano a wani liyafa da aka yi masa na karrama shi a matsayinsa na Asiwaju na Yarbawa a Kano.
“Lokacin da mace take naƙuda don ta haihu zafi yana da yawa. Ka ga, idan ka duba siyasar da gwamnatin Tinubu ta gindaya, mu ba shi akalla shekaru biyu. Na san lokaci mai tsawo ne mutum bai ji dadin komai ba, amma a cikin kasa da shekaru biyu za ku ga tasirin, tattalin arzikin zai canza.”
abejide ya ce shugaba Tinubu kwararre ne kan harkokin kudi wanda ya san abin da zai yi domin samun sakamakon da ake bukata.
Kalaman dan majalisar na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan Najeriya da dama ke nuna rashin jin dadinsu da tsadar rayuwa.
Kididdigar farashin kayan masarufi da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar ta nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki a cikin watan Disamba ya kai kashi 28.92 daga kashi 28.20 da aka samu a watan Nuwamba 2023.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Dan Majalisa Ya Roki Yan Najeriya a Bawa Tinubu Shekara Biyu Ya Gyara Tattalin Arzikin kasar”