Dambarwar ASUU: Kotu ta nuna ingancin dokar “Babu Aiki Babu Biya”

Kotun ma’aikata ta inganta hukuncin gwamnatin tarayya kan dokar “Babu aiki babu biya” a karar da ita gwamnatin tarayya ta shigar da kungiyar Malaman jami’o’in Najeriya (ASUU).
A yayin sauraron karar, Mai shari’a Banedict Kanyip ya bayyana cewa dokar da gwamnatin ta yi amfani da shi kan malaman jami’o’in a shekarar da ta gabata na Babu Aiki Babu Biya ya inganta a hukumance.
Kotun ta ce gwamnati na da ikon rike albashin ma’aikata a yayin da suka fantsama yajin aiki.
Sai dai kuma ta kara da cewa, ya saba ma ‘yancin jami’o’I a kakaba musu sabuwar tsarin biyan albashi na IPPIS. Kotun ta bayyana cewa jami’o’I na da ‘yancin zabar irin tsarin biyan albashi da ya fi kwanta musu a rai ba tare da samun tsaiko daga gwamnati ba. Don haka su na da yancin zabar UTAS a madadin IPPIS.
Kungiyar ASUU dai ta tsunduma yajin aiki ne a watan Fabrairun bara, inda suka shafe kusan watanni goma, a sabili da hakan ne gwamnatin tarayya ta ki amincewa da biyan malaman albashin su na adadin watannin da basu yi aiki ba.