December 7, 2021

Dalilan Sulhun Imam Hasan Da Mu’awiya

Cigaba daga rubutun da ya gabata kan tarihin imam Hassan (as)

Wannan yanayin da ya kewaye Imam Hasan (a.s.) ya yi mummunan kuntata matsayinsa ta fuskar da irinsa ya karanta a tarihi. Domin rundunar da yake shugabanta ne bala’in ya lullube, wasu kazamai lalatattu suka kutsa kai cikinta, ta yadda har (rundunar) ta kusa mika Imam Hasan a hannun makiyansa, al’ummar da ya dogara da ita kuma yake yi mata tsari don gaba kuma yake jagorancin tafiyarta ne ta canza hanyarta zuwa abin da zai amfani abokan gaba, wannan kuwa ta hanyar tasirantuwa da farfagandoji da rudarwa da watsa kudi; da haka ma’aunin karfin daularsa ya sauya zuwa abin da zai taimaki Umayyawa.

Hakika Mu’awiya ya tura dukiya mai yawa zuwa shugabannin kabilu da masu tasiri a cikin mutanen Iraki, ya barnatar da kudin da samun irin haka ya karanta, da haka ya bata kokarinsu, ya raunana zukatansu; sai suka juya baya daga kudurinsu na bin Imam Hasan (a.s.) wajen yakar Mu’awiya, har wasu suka sanar da wilayarsu da biyayyarsu ga Mu’awiya, suka yi masa alkawarin cewa za su kawo masa Imam Hasan a matsayin fursunan yaki ana shiga fagen fama idan yaki ya yi zafi.

Wannan ya haifar da ha’incin Ubaidullah bin Abbas, kwamandan rundunar Imam a bataliyar nan ta gaba, inda ya koma ya hade da Mu’awiya tare da kusan kashi biyu bisa uku na sojojin da ke bataliyarsa, bayan ya karbi rashawa mai tsoka daga Mu’awiya.

Ta hanyar dabaru, makirce-makirce da rashawarsa, Mu’awiya bai damu da a zubar da kowane irin jini ko a kashe rayuka ba, matukar dai zai cimma bukatunsa.

A gefe guda kuma, Imam Hasan (a.s.) na gudanar da abubuwa ne da ruhin imaninsa madaukaki. Ya kasance yana nisanta daga makirci da kisan mummuke, ba ya son ya shiga cikin yakin da ba shi da amfani wajen tabbatar da gaskiya da adalci.

A irin wannan yanayi, ba wata fa’ida ga yakin da ba zai haifar da komai ba face murkushe abin da ya saura na muminai. An ruwaito Imam Hasan (a.s.), yayin da ya ke bayyana dalilin sulhun, yana cewa:

Wallahi da na yaki Mu’awiya da sun riki wuyana har sun mika ni zuwa gare shi cikin ruwan sanyi. Wallahi in yi sulhu da shi ina madaukaki ya fi min a kan ya kashe ni ina fursunan yaki; ko ya yi min gori, (hakan) ya zama abin zagi ga Banu Hashim”.

Ya kara da cewa:

Lallai ni na ji tsoron a tsige Musulmi daga doron kasa, sai na so ya zama akwai wani mai kira zuwa ga addini”.

Ban zama mai kaskantar da Muminai ba; sai dai ni mai daukaka su ne. Ba wani abu na yi nufi da sulhuna ba face kau da kisa daga gare ku yayin da na ga sandar Sahabbaina da nokewarsu daga yaki”.

Har ila yau ya taba fadawa Abu Sa’id cewa:

Ya kai Abu Sa’id! Dalilin sulhuna da Mu’awiya shi ne (irin) dalilin sulhun Manzon Allah da Bani Dhamrah da Bani Ashaja’a da mutanen Makka, a lokacin da ya koma daga Hudaibiyya.

SHARE:
Raruwar Magabata 0 Replies to “Dalilan Sulhun Imam Hasan Da Mu’awiya”