July 31, 2021

WASU DALIBAN MAKARANTAR FGC YAURI SUN KUBUTA DAGA SANSANIN MASU GARKUWA DA MUTANE

Daga Yakub Ismai’l

 

Wasu dalibai guda biyu na makarantar sakandire ta FGC Yauri dake jihar Kebbi sun samu kubuta daga sansanin masu garkuwa da mutane.

Rahoto ya tabbatar da cewa bayan sun share tsahon lokaci suna gudun ceton rai, sun tsinci kansu a kauyen Dandalla  dake kusa da garin Dansadau. Isar su garin sun galabaita sosai, wasu daga cikin mutanen garin sun taimaka inda suka boyesu sannan daga bisani suka mika su ga Ofishin ‘yan sanda dake kusa da su.

Lamarin garkuwa da su din ya faru ne tun cikin watan Yuni yayin da masu garkuwa da mutanen suka shiga makarantar a kan Babura kana kuma suka yi awun gaba da dalibai a kalla 30 da kuma malamai guda uku.

Bayan mutanen garin sun mika su Ofishin ‘yan Sanda, daga bisani an daukesu zuwa Gusau domin tattara bayanai.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “WASU DALIBAN MAKARANTAR FGC YAURI SUN KUBUTA DAGA SANSANIN MASU GARKUWA DA MUTANE”