August 9, 2021

Dakarun Кungiyar Hizbullah Sun Sake Jaddada Mubaya’arsu Ga Sayyid Nasrallah

Daga Jaridar “Hausa Radio Iran”

Dakarun ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon sun sake jaddada mubaya’arsu ga shugaban ƙungiyar Sayyid Hasan Nasrallah.

A wani faifan bidiyo da tashar talabijin ɗin Al-Manar mallakin ƙungiyar ta watsa, dakarun ƙungiyar sun bayyana cewar suna nan daram kan biyayyarsu ga shugaban na su, wato Sayyid Nasrallah, suna masu cewa a duk lokacin da ya ba su umurni a shirye suke su aiwata ba tare da wani ɓata lokaci ba.

A cikin faifan bidiyon an jiyo dakarun suna faɗin cewa: A duk lokacin da ka ba da umurni, mun har wasu makamai masu linzami, kuma Allah Ya ba mu nasara ƙarƙashin sanya ido da kuma kulawarka.

Dakarun suna ishara ne da makamai masu linzamin da suka harba cikin ‘Isra’ila’ a ‘yan kwanakin baya a matsayi mayar da martani ga wuce gonan Isra’ilan ga Kudancin Labanon inda suka ce sun harba rokoki ba tare da makaman kariya na ‘Isra’ilan sun iya kakkaɓo su ba.

Har ila yau dakarun sun sake jaddada aniyarsu ta ci gaba da riƙo da tafarkin gwagwarmaya, suna masu jaddada cewa mutanen ƙauyukan Al-Arqoub da Hasbiya da ke Kudancin Labanon ɗin inda daga nan ne aka harba waɗannan rokokin sun kasance kuma za su ci gaba da kasantuwa abokan tarayyarsu cikin ayyukan gwagwarmaya.

Wannan sake jaddada mubaya’ar ta dakarun gwagwarmayar tana zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da dakarun na Hizbullah suka harba wasu makamai masu linzami zuwa ‘Isra’ilan’ sannan kuma shugaban ƙungiyar ta Hizbullah ya sake jaddada aniyar ƙungiyar na mayar wa ‘Isra’ilan da martani a duk lokacin da ta kawo wani harin wuce gona da iri cikin Labanon.

 

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “Dakarun Кungiyar Hizbullah Sun Sake Jaddada Mubaya’arsu Ga Sayyid Nasrallah”