November 19, 2022

Da yiwuwar FIFA ta hana sayar da giya a gasar kofin duniya a Qatar

 

Kasar Qatar mai masaukin baki a gasar cin kofin duniya, na matsa wa FIFA lamba kan ta dakatar da sayar da giya a filayen wasanni takwas da za a buga wasanni a ciki a cewar rahotanni.

Sayar da barasa abu ne da Qatar ke ɗaukar mataki sosai, amma kuma ana tunanin sayar da barasar a wasu gurare waje da filayen wasa da kuma wuraren da ƴan kallo ke taruwa, da kuma cikin otal-otal.

Kamfanin giya na Budweiser yana daya daga cikin manyan masu ɗaukar nauyin FIFA, amma an gaya masa a ranar Asabar da ya mayar da rumfunan sayar da barasar nesa da filayen wasa zuwa wasu zababbun wurare.

Jaridar Times ta ruwaito cewa Qatar 2022, na kokarin ma hana sayar wa kwata-kwata, inda a yanzu haka ana ci gaba da tattaunawa tsakanin FIFA da Budweiser.

Kamfanin dillancin labarai na PA ya tuntubi FIFA da mai Budweiser AB InBev don yin sharhi.

Dangane da bukatar matsar da kantunanta nesa da filayen wasa, AB InBev ya shaida wa Sky News cewa: “An sanar da AB InBev a ranar 12 ga Nuwamba, kuma yana aiki tare da FIFA don mayar da wuraren ba da izinin zuwa wurare kamar yadda aka umarce su.

©Daily Nigeria.

SHARE:
Labarin Wasanni 0 Replies to “Da yiwuwar FIFA ta hana sayar da giya a gasar kofin duniya a Qatar”