June 21, 2023

Da izinin kotu muke  tsare da Emefiele – Yan sandan farin kaya

 

Hukumar yan sandan farin kaya a jiya Talata ta nemi babbar kotun tarayyar Najeriya da ke Abuja da ta yi watsi dq karar da da tsohon gwamnan Babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya shigar gaban ta.

Tsohon gwamnan babban bankin dai ta hanyar Lauyansa Barista J.B Daudu ya nemi kotun da ta sahhale masa shakar iskar yanci inda ya nuna cewa hukumar yan sandan farin kaya na rike da shi ne ba bisa ka’ida ba.

Sai dai kuma hukumar ta yan sandan farin kaya ta nemi Kotun da ta yi watsi da bukatar lauyan Emefiele. Kana lauyan hukumar ta DSS wato I. Awo ya bayyana cewa garkame Emefiele an yi shi ne bisa tanajin doka sabida sun samu izini daga kotun Majastare dake birnin tarayya Abuja inda ta bada izinin cigaba da garkame tsohon gwamnan babban Bankin.

Shi dai tsohon gwamnan babban Bankin an damke shi ne a ranar 9 ga watan Yuni awanni kadan bayan da aka tsige shi daga mukamin sa. Hukumar yan sandan farin kaya na rike da shi inda ta ke zargin sa da laifuka da dama.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Da izinin kotu muke  tsare da Emefiele – Yan sandan farin kaya”