March 26, 2024

DA DUMI-DUMI: Rundunar Sojojin Najeriya za ta saki tubabbun ‘Yan Boko Haram 200

Rundunar sojin Najeriya na shirin sakin fursunoni sama da 200 da suka tuba kuma suka yanke alaka da kungiyar Boko Haram.

 

Sojojin sun kama mutanen da ake tsare da su ne a wasu  zafafan hare-hare da suka gudana.

 

Bincik ya nuna cewa za a mika su ga gwamnatin Jihar Borno domin su koma cikin al’umma yadda ya kamata.

 

Za a gudanar da taron wanke su ne a Barikin Giwa da ke garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno a safiyar ranar Talata.

 

“Akalla mutane 200 da ake zargin ‘yan Boko Haram ne da suka tuba jami’an tsaro za su wanke, kuma za a mika su ga gwamnatin jihar Borno domin gyara, nasiha da kuma mayar da su cikin jama’ar gari.

 

“An shirya bikin wanke su da safiyar yau (Talata) da karfe 10:00 na safe a Barikin Giwa,”.

 

Majiyar ta ce kwamishiniyar harkokin mata ta jihar, Zuwaira Gambo da takwararta ta yada labarai da tsaron cikin gida, Farfesa Tar Umar, za su karbi wadanda aka wanke a madadin gwamnatin jihar.

SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “DA DUMI-DUMI: Rundunar Sojojin Najeriya za ta saki tubabbun ‘Yan Boko Haram 200”