August 31, 2021

Da Dumi-Dumi: Kungiyar ASUU ta ce baza ta tafi yajin aiki ba

Daga Mohd Bakir
Rashin jituwa tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kungiyar malaman jami’a (ASUU) ya sake tsamari a yan kwanakin nan, wanda alamu suka nuna yiwuwar shiga kungiyar wani sabon yajin aiki.
Tuni dai daliban jami’a suka yi ta nuna tashin hankulan su, sakamakon hakan yakan shafi karatun su.
Labari mai dadi a yammacin nan ta Talata kungiyar ta ASUU ta bayyana janyewar aniyar ta, inda ta tabbatar cewa baza ta shiga wani yajin aiki ba.
SHARE:
Rahotanni 0 Replies to “Da Dumi-Dumi: Kungiyar ASUU ta ce baza ta tafi yajin aiki ba”