August 27, 2021

Cikar Jaridar Ahlul-Baiti Wata Guda

Yau juma’a, Jaridar AHLULBAITI Online da aka fara wallafata take cika wata guda, an fara gudanar da itane a ranar idi mai girma (Wato ranar Gadir) ranar  da manzon Allah (S) ya nasabta Imam Ali (AS) a matsayin khalifa kuma wasiyyi a bayan sa, a irin wannan babban rana aka fara gudanar da ita, wanda Alhamdulillah zamu iya cewa Jaridar AHLULBAITI kwalliyace da zata biya kudin sabulu da izinin Allah.

 

Jaridar ta AHLULBAITI Online ta kunshi janibobi daban daban, akwai janibin Rayuwar magabata, akwai kuma janibin Tambayoyin fikihu wanda Hujjatul Islam Sheikh Nur Dass (H) yake amsawa, akwai kuma rayuwar iyali a musulunci na babban Malamin nan Sheikh Bashir lawal wanda akafi sani da sautush-shi’a, akwai kuma tsokaci na Sheikh Saleh Zaria, haka nan akwai Makala, akwai labarin wasanni,da labaran duniya, tarbiyyan yara da asasi wacce itace Akida.

 

Mun sami sakonnin ‘yan uwa da dama da suka shafi gyara, da masu yi mana fatan alheri, kuma alhamdulillah sakon ku ya iso garemu, mun sami sakon Malam Mujtaba Adam, Malam Auwal Bauchi,Muhammad Bakir Muhammad, Malam Muhammad Ahmad Suleiman, Malam Dalhatu Ibrahim, Malam Ya wali Rabilu kaima munga sakon ka, haka nan munga sakon Malam Ali Maina Abubakar, Haka kaima Malam Baba Abdukadir, haka Muhammad Bashir Ibrahim, Malam Aliyu Lawal kaima mun sami sakon ka, haka kaima Malam Aliyu kubau, haka kema maman Ahmad S kura, Haka munga sakon Malam Muhammad Headmaster da Malam Nata’ala Muh’d, bazamu manta dakai ba Malam yakub salisu kaima munga sakon ka dama sauran wadanda bamu ambaci sunayen su ba.

 

‘Yan uwa masu girma ma’abota karanta wannan jarida ta AHLULBAITI Online muna sanar daku cewa kofa abude take ga duk wani gyara da za’ai mana, da duk wani rubutu da za’a aiko mana koda kuwa rahotanni ne a shirye muke mu karba, mu tantance kuma mu buga shi a wannan jarida taku.

 

Fatan mu shine wannan jarida ta zamto dalilin hadin kai tsakanin dukkan al’ummu musamman musulmi, Allah ya datar damu Amin.

 

~ Zaku iya aiko mana sakonni ta email din mu: ahlulbaiti2021@gmail.com

~ Zaku kuma iya ziyartar shafin mu na Fazbuk wato Jaridar Ahlulbaiti Online.

 

~ Ga mai bukatar manhajar jaridar mu kuma zai ya turo mana sako  ta watsap da wannan number +234 708 979 3590 ko kuma ya turo mana sako ta shafin mu na fazbuk.

 

SHARE:
Makala 0 Replies to “Cikar Jaridar Ahlul-Baiti Wata Guda”