June 21, 2023

China Ta Bayyana Kalaman Amurka Akan Shugabanta Da Cewa; Ba Ta Da Ma’ana Kuma Tsokana

 

Ma’aikatar harkokin wajen kasar China ta ce kalaman da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya bayyana shugaban China da cewa; Dan kama-karya ne, suna a matsayin tsokana.

Ma’aikatar harkokin wajen na kasar China ta bakin mai Magana da yawunta Mao Ning wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Laraba, ya bayyana cewa: Babu ladabi ko kadan a cikin kalaman na shugaban kasar Amurka, kuma ya fusata China matuka.

Joe Biden wanda ya gabatar da jawabi a yayin wani taro a Arewacin California ya ce: Harbo balo-balo din China da Amurka ta yi a watan Fabriaru, ya bata wa shugaban kasar China rai matuka.

Shugaban kasar na Amurka ya kara da cewa; Shugaban kasar na Amurka ya kuma ce; Shugaban kasar ta China ya fusata ne saboda balo-balo din da aka harbo tana kunshe da akwatuna biyu masu dauke da bayanan asiri. Da gaske nake, haka ‘yan kama karya suke saboda ba su san abinda yake faruwa ba.”

Shugaban na kasar na Amurka ya yi wannan zancen ne dai kwana daya bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blenken ya kai ziyara kasar ta China a wani kokari na dinke barakar dake tsakanin kasashen biyu.

Sai dai bayan wannan kalaman, wata sabuwar rashin fahimtar junan ta sake kunno kai a tsakanin kasashen biyu.

SHARE:
Labaran Duniya 0 Replies to “China Ta Bayyana Kalaman Amurka Akan Shugabanta Da Cewa; Ba Ta Da Ma’ana Kuma Tsokana”